Jami’in Makamashin Nukiyar Iran Ya Ce; Zarge-Zargen Da Ake Yi Kan Shirin Makmashin Nukiliyar Iran Siyasa Ce Kawai
Published: 10th, June 2025 GMT
Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa
Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba.
Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba.
Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun nan, sun samo asali ne daga matsin lamba na siyasa da nufin tilastawa Iran yin watsi da nasarorin da ta samu.
Ya ci gaba da cewa: Martanin Iran kan duk wani kuduri da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa za ta yi kan Iran zai hada da matakan fasaha, kuma martanin Iran ga hukumar zai hada da sake tantance hadin gwiwar da take bai wa hukumar.
Behrouz Kamalvandi ya yi nuni da cewa: Yayin da nasarorin da Iran ta samu a fannin kimiyya ke ci gaba, za a kara matsin lamba ta siyasa don kawar da kasar daga kan tafarkinta, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba ga wannan matsin lamba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce: Rashin Dakatar Da Uranium Da Dage Takunkumi Sune Hanyar Warware Takaddamar Da Ita
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana iya cimma shi cikin sauri.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafinsa na Twitter game da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da kuma matsayin Iran a kansu yana mai cewa: Shugaba Trump ya bayyana a lokacin da ya shiga fadar White House cewa ba lallai ne Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, wannan matsayi ya yi daidai da akidar Iran ta nukiliya, kuma za a iya la’akari da shi a matsayin tushen yarjejeniyar da za a iya cimmawa.
Ya kara da cewa: A yayin da ake ci gaba da tattaunawa a ranar Lahadi, a bayyane yake cewa yarjejeniyar da za ta tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a shirin nukiliyar Iran na kan hanya, kuma za a iya cimmawa cikin gaggawa.