NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya
Published: 10th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
’Yan Najeriya suna ci gaba da nuna damuwa da yadda rahotannin kwace-kwacen waya suke karuwa a sassan daban-daban na kasa.
Daya daga cikin rahotanni na baya-bayan nan shi ne inda a birnin Kaduna aka bayar da rahoton cewa wani matashi ya daba wa wani babban soja wuka saboda jami’in ya ki ya mika wayarsa.
Ko me mahukunta suke yi don hana aikata wannan laifi?
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin SallahWannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hana kwacen waya Kwacen waya
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu sake gina kasuwar waya ta Farm Center — Abba
Gwamnan Kano Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar.
Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban IranSanarwar ta ce bayan ziyarar gani da ido da gwamnan ya yi a ranar Juma’a, ya ɗauki matakin sake gina kasuwar tare da sabunta ta da zamanantar da ita, aikin da da ya ce “gwamnan zai kashe naira biliyan 2.”
“Wannan yunƙuri ba kawai saboda gobarar ba ce, za mu yi amfani da wannan damar ne domin inganta tattalin arzikin jihar, da samar da ayyukan yi,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta saya ƙarin fili domin faɗaɗa kasuwar, inda za ta samu damar gina abubuwan da ake buƙata a kasuwa na zamani, ciki har da gina sashen masu kashe gobara domin jiran kar-ta-kwana.
“Ba kasuwa kawai za mu gina ba, cibiyar kasuwanci za mu gina domin jawo ’yan kasuwa daga ƙasashen duniya,”in ji shi.