An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe
Published: 12th, June 2025 GMT
A yayin da ake tsaka da bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya, al’ummar jihar Gombe sun wayi gari da sabuwar dokar takaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe a duk faɗin jihar.
Sanarwar da ta fito ne daga hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, DSP Buhari Abdullahi, ranar Alhamis, a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar Bello Yahaya.
Sanarwar ta ce an kafa dokar ne don rage ayyukan ta’addanci a fadin jihar.
Guguwa ta hallaka mutum 6, ta jikkata 30 a Taraba An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a FilatoKafa dokar na zuwa ne kwana uku bayan wasu matasa da ba a tantance su wane ne ba suka kashe wani magidanci mai suna Ahmad Aliyu, wanda aka fi sani da Amadi Kasiran, a unguwar Hammadu Kafi da ke Gombe, a daren Lahadi.
Sanarwar ta ƙara da cewa duk wanda aka kama ya karya dokar zai fuskanci hukunci mai tsauri, ciki har da gurfanar da shi a gaban kotu.
Kazalika, sanarwar ta ce dokar ta haramta ɗaukar mutum fiye da ɗaya a kan babur domin rage matsalar rashin tsaro a jihar.
“Dokar hana hawa babur da goyon biyu ta fara aiki ne daga yau, Alhamis, ranar bikin Dimokradiyya, har sai wani lokaci da ba a kayyade ba,” in ji Kakakin ’yan sandan.
Rundunar ’yan sandan ta ce an ɗauki wannan mataki ne don magance matsalar bata-gari na ‘’yan kalare’ da sauran ayyukan ta’addanci.
A lokacin da wakilinmu ya kai ziyara kwaryar birnin Gombe, filin wasa na Pantami ya kasance a rufe ba tare da alamar wani biki ba.
Sai dai ya gane wa idanunsa cewa an jibge jami’an tsaro a sassa daban-daban, ciki har da ’yan sanda, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), da kuma ’yan banga.
Wannan sabuwar doka ta ja hankalin mutane da dama a jihar, musamman mazauna yankunan da aka fi samun matsalar tsaro.
Sai dai wasu na gani za ta kara jefa jihar cikin kuncin talauci sakamakon rufe shaguna da kasuwanni da wuri saboda rashin abun hawa wanda dama can baburan aka fi hawa saboda tsadar rayuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Hawa babur
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.