Kotu ta yi fatali da bukatar Akpabio, ta umarce shi ya biya Natasha N100,000
Published: 11th, June 2025 GMT
Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da bukatun Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sannan ta ci shi tarar Naira 100,000.
Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Hamman Barka dai ta yi watsi da bukatun ne kan karar da aka shigar ranar 21 ga watan Mayun 2025, bayan neman bukatar janye karar da aka daukaka.
Bukatun dai na kunshe ne a cikin wasu kararraki masu lamba CV/395/M1/2025 da kuma CV/395/M2/2025, wadanda aka shigar a ranakun uku da kuma 25 ga watan Mayun 2025, wanda a cikinsu aka ambaci sunan Akpabio a matsayin mai daukaka kara.
DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Rikicin Filato: An sake kone gidaje 96 a ManguWadanda ake kara kuma su ne Sanata Natasha da Magatakardar Majalisar Dokoki ta Kasa da Majalisar Dattawa da shugaban kwmaitin da’a, ladabtarwa da korafe-korafen jama’a na majalisar, Sanata Neda Imasuem.
Tun farko dai a cikin karar, Akpabio ya nemi kotun da ta kara masa lokacin da zai iya kalubalantar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke mai lamba FHC/ABJ/CS/384/2025, wanda ta yanke ranar 10 ga watan Maris 2025 bisa hujjar cewa akwai kura-kurai a cikinsa.
Sai dai da take yanke nata hukuncin, kotun ta ce ta amince da bukatar janye kararrakin guda biyu, kamar yadda mai kara ya bukata.
Sai dai ta ce ta ci mai karar tara Naira 100,000, wadanda za a ba wacce aka yi kara.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq.
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoSun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi.
A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Saudiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da cikakken goyon baya wajen ganin an saki waɗanda aka kama.
Bincike ya gano cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, suka ƙwayoyin a jakunkuna waɗanda aka kama.
Mutanen uku da aka kama, sun tashi a jirgin Ethiopian Airlines a ranar 6 ga watan Agusta don yin Umara, amma aka kama su a Saudiyya.
Binciken NDLEA ya kai ga kama wani shugaban masu safarar miyagun ƙwayoyin, mai shekaru 55, Mohammed Ali Abubakar (wanda aka fi sani da Bello Karama).
Hakazalika, hukumar ta kama wasu mutum uku ciki har da ma’aikatan jirgi.
Mutanen da aka kama su ne suka shirya safarar ƙwayoyin a jakunkunan mutane da aka kama a Saudiyya.
NDLEA ta gabatar da shaidun da suka tabbatar da cewa mutanen da aka kama a Saudiyya ba su da laifi.
Sakamakon haka, hukumomin Saudiyya suka sako ɗaya daga cikinsu a ranar 14 ga watan Satumba, sannan suka sako sauran biyun a ranar 15 ga watan Satumba.
Babafemi, ya ce Marwa ya gode wa hukumomin Saudiyya saboda mutunta yarjejeniyar haɗin kai tsakaninsu da Najeriya.
Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Shari’a, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Mai Bai Wa Shugaba Shawara Kan Harkar Tsaro, saboda gudummuwarsu.
Ya ƙara da cewa wannan lamari ya nuna cewa Najeriya tana tsayawa wajen kare ‘yan ƙasarta a ƙasashen waje kuma ba za ta yadda wani ɗan Najeriya ya sha wahala saboda laifin da bai aikata ba.