Aminiya:
2025-05-30@01:54:36 GMT

Ba zan daina sukar gwamnatin Tinubu ba — Farfesa Yusuf

Published: 13th, February 2025 GMT

Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya zargi Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin hana shi magana sakamakon sukar manufofinta da yake yi.

Yusuf, wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar gwamnati, Hukumar EFCC ta kama shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin rashawa.

HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Haruna Zago a Kano Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’

Sai dai ya musanta dukkanin zarge-zargen, inda ya ce an shirya masa tuggu ne saboda dalilan siyasa.

Da yake magana yayin da yake tsare a gidan gyaran hali na Kuje, ya ce, “Wannan wani yunƙuri ne na hana ni yin magana kawai. Zarge-zargen EFCC ba su da tushe balle makama, kuma suna amfani da tsoffin maganganu marasa tushe.

“Ina da ƙwarin gwiwa cewa lauyoyina za su kare ni.”

Farfesa Yusuf ya kuma zargi jami’an tsaro da bibiyarsa da iyalansa.

“Tun tsawon watanni suke bin diddigin rayuwata, a zahiri da kafafen sada zumunta.

“Wannan gwamnati na amfani da hanyoyin danniya domin hana jama’a faɗin albarkacin bakinsu, kamar yadda aka saba a zamanin mulkin soja,” in ji shi.

Kama shi ya jawo ce-ce-ku-ce daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da kuma ’yan adawa, waɗanda suka bayyana hakan a matsayin yunƙurin muƙushe ’yancin faɗin albarkacin baki.

Wasu masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam, sun buƙaci a saki Yusuf nan take, inda suka ce suka da adawa ga manufofin gwamnati bai kamata a ɗauke su a matsayin laifi ba.

“Dimokuraɗiyya na buƙatar ra’ayoyi mabambanta. Amfani da tsoratarwa da shari’a don hana masu suka magana babbar barazana ce ga ’yancin jama’a,” in ji wani mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam.

Duk da kasancewarsa a tsare, Yusuf ya yi alƙawarin ci gaba da magana kan yadda gwamnatin Tinubu ta gaza.

Ya buƙaci ’yan Najeriya da su zama masu lura da kuma neman haƙƙinsu a wajen gwamnati.

“Wannan ba batuna ne ni kaɗai ba. Batun kare ’yancin jama’a ne da hana kowace gwamnati amfani da tsoro don muƙushe al’umma.

“Dole mu tashi tsaye don kare haƙƙoƙinmu,” in ji shi.

Yanzu haka dai yana tsare yayin da kotu ta ɗage zaman sauraron buƙatar bayar da belinsa zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Farfesa Usman Yusuf gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

Ranar Yara: Yaran Nijeriya Farin Ciki Za Su Yi Ko Baƙin Ciki?

Ga shi abin ci ya yi tsadar da samun a ci sau uku yana da wajala, balle kuma a nemi mai gina jiki. Kwananan masu sayar da ƙwai suka koka saboda rashin ciki, masu kifi dai haka abin yake balle kuma masu nama.

Duk da hakan bai hana yara murmushi ba wataƙila saboda ba su da masaniyar irin wahalar da iyayensu ke sha wajen ganin sun samar musu da rayuwa mai inganci.

Lallai ya kamata ƴan majalisa su matsala ƙaimi a samar da wani yanayi ga yara musamman wajen kare su daga faɗawa ƙangin talla ko bautar aikatau ko kuma zama ƴan jagorar masu bara, hakan kuwa zai faruwa ne idan aka aiwatar da dokar kare ƴancin yara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Atiku Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu, Ya Yi Gargaɗi Kan Cin Sabon Bashi
  • Sin Na Maraba Da Kamfanonin Kasa Da Kasa Har Da Na Amurka 
  • Yadda Rashin Ɗaukar Wani Maniyyaci Ya Hana Jirgi Tafiya Har Sai Da Ya Dawo Ya Ɗauke Shi
  • Amurka za ta hana ‘’visa’’ ga daliban dake sukanta a shafukan sada zumunta
  • Trump Ya Gargadi Natanyahu Kan Kokarin Hana Tattaunawa Da Iran Tafiya
  • Kungiyar Amnesty Tana Zargin : Gwamantin DRC Da Kungiyar M23 Da Yiyuwar Aikata Lafukan Yaki
  • Ina Fatan Cigaba Da Taka Leda Har Zuwa Lokacin da Zan Cika Shekara 40 A Duniya – Salah
  • Gwamnati Ta Kammala Samar Da Fasfo Sama Da 200,000 Da Suka Yi Jinkiri
  • Hukumar Kare Hakkin Bil’adam Ta MDD Ta Bukaci A Kawo Karshen Kissan Kiyashi A Gaza
  • Ranar Yara: Yaran Nijeriya Farin Ciki Za Su Yi Ko Baƙin Ciki?