Birgadiya Janar Rasul Sanaei-Rad wanda shi ne babban kwamandan sojan kasa na Iran ya bayyana hakan ne a wurin tunawa da zagayowar ranar ‘yanto da garin Khurramshahr daga mamaya sojojin Ba’asiyya na Sadam, a lokacin kallafaffen yaki.

Birgediya janar Sanaei -Rad ya kuma yi ishara da ‘yanto da garin na Khurramshar yana mai kara da cewa; yadda al’ummar Iran su ka yi gwagwarmayar ‘yanto da garin Khurramshahr, bayan tsawon shekaru 8 na yaki, ya sa Amurka ta fahimci cewa yaki da Iran yana da tsada da kuma hatsari; kuma da ace sun san za su yi nasara ta hanyar karfin soja da ba su zauna akan teburin tattaunawa ba.

Janar Sanaei ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su yi tsayin daka wajen fuskantar Amurka da wuce gona da irinta, kamar yadda su ka yi a lokacin yakin tsaron kasa mai tsarki wanda ta dauki shekaru takwas ana yi, da kasashen turai su ka goyi bayansa.

Haka nan kuma ya yi kira da a kare cigaban da aka samu a fagen fasahar makamashin Nukiliya.

Birgediya janar Sanaei-Rad ya kuma ce; Kare karamarmu a wannan lokacin da kuma manufofinmu na nan gaba, suna tana tattare da yin gwagwarmaya.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu

Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan  sahayoniyya kan kasar Iran

Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren.

Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari.

A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a ranar talata mai taken “Hanyar Haramtacciyar kasar Isra’ila kan Iran: Abubuwan da za a samu a nan gaba,” Sajjadpour, yayin da yake magana kan halaye da matsayin Turai a yakin kwanaki 12 da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan Iran, ya ce: “Turai na goyon bayan gwqwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila a kodayaushe, kuma shiru ko goyon bayan da wasu kasashen Turai suka yi kan zaluncin Isra’ila za su kasance da sun mummunar tasiri a cikin zukatan Iraniyawa.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Musanta Neman Ci Gaba Da Gudanar Da Tattaunawa Da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
  • Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliya Kasar Idan Tanaso
  • Iran Ta Tabbatar Da Cewa Tana Iya Yakar Amurka Da HKI A Lokaci Guda
  • A Karon Farko HKI Ta Yi Furuci Da Cewa Iran Ta Kai Wa Cibiyoyinta Na Soja Hare-hare
  • Iran Za Ta Yi Nazarin Sabuwar Gayyatar Da Amurka Ta Yi Mata Na  Sabuwar Tattaunawa
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce; An Rusa Hanyar Tattaunawa da Iran Kan Shirin Na Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
  • Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos