Guterres: MDD Ba Za Ta Shiga Duk Wani Shiri Da Ba Zai Girmama Dokokin Kasa Da Kasa Ba A Gaza
Published: 24th, May 2025 GMT
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani tsari da ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba a Gaza.
Bayanin nasa dai ya zo ne a matsayin mayar da martani akan maganar da ta fito daga HKI na cewa tana aiki tare da Amurka domin raba kayan agaji a Gaza.
Babban magatakardar MDD ya kuma kara da cewa; kaso 80% na yankin Gaza, ko dai yana karashin mamayar Isra’ila da kuma wanda aka bai wa mazaunansa umarnin su fice daga cikinsa.
Antonio Guterres ya yi gargadin cewa matukar ba a bude iyakoki ba, aka kuma shigar da kayan agaji, to mutanen Gaza za su rasa rayukansu.”
Babban magatakardar MDD ya tunawa HKI cewa, a matsayinta na ‘yar mamaya, wajibi ne ta mutunta fararen hula da kare karamarsu kamar yadda dokokin kasa da kasa su ka tanada.”
Haka nan kuma ya yi kira da a dakatar da yaki a cikin gaggawa,kuma wajibi ne a yunkura a yanzu domin a kowace rana ana kara samun wadanda suke rasa rayukansu da kuma jikkata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA