An Kaddamar Da Bikin Baje Kolin Aikin Gona Na Kasa Da Kasa Na Cote d’Ivoire
Published: 24th, May 2025 GMT
An kaddamar da bikin baje koli na aikin noma da albarkatun dabbobi na kasa da kasa karo na 7 na kasar Cote d’Ivoire a cibiyar bukukuwan baje koli ta kasa da kasa dake birnin Abidjan, a jiya Jumma’a 23 ga wannan watan.
A matsayin muhimmiyar bakuwar kasa a gun bikin baje kolin, kasar Sin ta kafa rumfarta a tsakiyar cibiyar, inda aka gwada fasahohin zamani na aikin noma da injuna na kasar Sin.
Firaministan kasar Cote d’Ivoire Robert Beugre Manbe, ya bayyana a yayin bude bikin cewa, kasar Sin tana kan gaba a duniya a fannin fasahohin zamani na aikin noma. Kuma kasar Cote d’Ivoire za ta ci gaba da yin kirkire-kirkire kan fasahohin zamani don sa kaimi ga zamanantar da aikin noma a kasar da kuma inganta karfinta a wannan fanni.
Mataimakin ministan harkokin aikin noma da raya kauyuka na kasar Sin Zhang Xingwang, ya bayyana cewa, kasar Cote d’Ivoire ta fi samar da cocoa da dan yazawa (cashew nuts) da roba da sauran amfanin gona, kuma kasar Sin tana da babbar kasuwa, don haka bangarorin biyu suna da kyakkawar makoma kan hadin gwiwar fasahohin aikin noma, da samar da amfanin gona, da tattalin arziki da cinikayya da sauransu. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Cote d Ivoire
এছাড়াও পড়ুন:
Malamin Addinin Musulunci Yayi Kira Da Ayi Gaggawa Gyaran Hanyar Zamfara
Wani malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Mohammed Tukur Sani Jangebe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta gudanar da kananan gyare-gyare daga mahadar Maru –Mayanchi – Maradun, da ke kan hanyar zuwa wani yanki na karamar hukumar Talata Mafara.
Ya ce mummunan yanayin hanyar yana ci gaba da haifar da babban kalubale ga matafiya tare da fallasa su ga hare-haren ‘yan bindiga a kan hanyar.
Sheikh Jangebe ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon Najeriya a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Ya bayyana cewa babbar hanyar Maru zuwa Talata Mafara ta samar da ramuka sama da dari, wadanda ke hana zirga-zirgar ababen hawa.
A cewarsa, hanyar ta zama hanya mai hatsarin gaske saboda yawaitar ‘yan fashi da garkuwa da mutane.
Malamin ya bayyana cewa, duk da cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar tagwayen hanya na titin Zaria zuwa Funtua zuwa Gusau zuwaTalata Mafara zuwa Sokoto amma har yanzu aikin bai kai ga tsallaka babbar hanyar Maru zuwa Talata Mafara ba.
Sheikh Tukur Jangebe ya bayyana cewa, dubban matafiya sun dogara ne da hanyoyin sufuri, kasuwanci, kiwon lafiya, noma, ko sauran muhimman ayyuka yayin da hanyar ita ce babbar hanyar da ta tashi daga Zamfara zuwa Sokoto har zuwa jihar Kebbi.
“Abin takaici, hanyar da ta tashi daga Bungudu ta bi ta Maru, Mayanchi, mahadar Maradun, har zuwa wani yanki na Talata Mafara, gaba daya ta lalace.
Sheikh Jangebe ya jadadda cewa, rashin kyawun hanyar yana haifar da fasa-kwaurin manyan motoci a lokuta da dama da kuma kara yawan yin garkuwa da mutane, domin masu aikata laifuka suna amfani da jinkirin da aka samu wajen yi wa matafiya kwanton bauna.
A cewarsa, direbobin ‘yan kasuwa da sauran masu ababen hawa na iya shaida rashin kyawun hanyar.
“Ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya da ta gaggauta gudanar da kananan gyare-gyaren gaggawa a kan hanyar domin saukaka radadin mutanen da ke tafiya a cikinta a kullum.”
Sheik Tukur Sani Jangebe ya kuma ce shigowar damina ta bana ya kara ta’azzara yanayin hanyar, tare da samar da karin ramuka da kuma sanya tafiye-tafiyen da ke da hadari.
Malamin ya kuma yi kira ga Gwamnonin jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, da Sokoto da su hada kai tare da gyara duk wani bangare na babbar hanyar da ke bukatar kulawa cikin gaggawa, har sai an kai ga aikin da ake yi a bangaren domin sake gina shi na karshe.
Ya bukaci ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ’yan kwangilar da ke tafiyar da aikin hanyar da su hanzarta gudanar da aikin domin ganin an kammala shi a kan lokaci.
AMINU DALHATU