Maariv: Tattaunawa A Tsakanin “Isra’ila” Da Kasashen Afirka Ta Yi Nisa Akan Hijirar Mutanen Gaza
Published: 24th, May 2025 GMT
Jaridar “Maariv” ta buga labarin da yake cewa; Tattauanwa a tsakanin “Isra’ila” da kasashen Afirka akan yadda za su bayar da dama ga mutanen Gaza da su yi hijira zuwa can, ta yi isa sosai.
Rahoton jaridar na jiya Juma’a ya ci gaba da cewa; Tattaunawar ana yinta akarkashin damar da za a bai wa Mutanen Gaza su yi hijira cikin zabin kansu, zuwa wasu kasashen na Afirka, kuma Amurka tana cikin wadanda ake tattaunawar da ita da wadannan kasashen na Afirka.
Tattaunawar dai ta kunshi yadda za a gina matsugunan Falasdinawan da za su yarda su yi hijirar, da kuma makarantunsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Za’a Gudanar Da Tattaunawa Zagaye Na 5 Tsakanin Amurka Da Iran A Ranar 23-Afrilu A Roma
Ministan Harkokin wajen kasar Omman ya bada sanarwan cew za’a gudanar da tattaunawa zagaye na 5 tsakanin Iran da Amurka kan shirin Iran na makamshin nukliya a ranar 23 gawatan Mayun da muke ciki a birnin Roma nakasar Italiay.
Tashar talabijin ta Presstv a nnan Tehran ta ce Har yanzun ba’a ji tabakin kasashen biyu ba bayan wannan sanarwan.
Sai dai kafin haka Iran tace tana tunanin dakatar da halattan taron saboda yadda jami’an gwamnatin kasar Amurka suka bayyana cewa duk wata yarjeniya da Iran sai ta hada da hana ta tace Uranium.
Amma iran ta dage kan cewa ba zata bar hakkinta wanda yarjeniyar NPT ta bata ba na tashe Uranium karkashin kula na hukumar IAEA ba.