Ministan Gine-Ginen Hanyoyi Na Kasar Iran Tana Kasar Iraki Don Kula Da Aikin Layin Dogo
Published: 25th, May 2025 GMT
Ministan gina hanyoyi da ci gaban kasa na JMI Farzaneh Sadegh ta ziyarci kasar Iraki don bin duddugin aikin layin dogo da ake ginawa tsakanin kasashen biyu.
Farzaneh Sadegh ta isa bienin Bagdaza a jiya Asabar inda mataimakin ministan sifiri na kasar Iraki da kuma jakadan kasar Iran a Bagdaza suka yi maraba da ita.
Ministan ta ziyarci inda sojojin Amurka suka kashe kwamandojin yaki da yan ta’adda Janar Kasim Sulaimani da kuma Mahdi Almuhandis a cikin watan Jenerun shekara ta 2020.
Farzaneh Sadegh zata gana da firai ministan kasar Iraki Mohammad shiaa Assudani, da wasu jami’an gwamnatin kasar Iraki. Sannan zata ziyarci aikin shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 33 wadanda kasashen biyu suke yi don hada garin Chalamce da birnin Basra ba kasar Iran, wanda zai bawa miliyoyin yan kasar Iran ziyarar wurare masu tsarki a kasar Iraki a ranakun 40 na Imam Hussain (a).
Tun shekara ta 2014 ne kasashen biyu suka so kammala aikin amma yan ta’adda suka hana aikin tafiya. Sannan aka sabonta yarjeniyar a shekara ta 2023 wanda ake saran aikin zai kammala kuma a fara aiki da layin dogon a Bana.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Iraki
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA