An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja
Published: 25th, May 2025 GMT
Jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama hakimin ƙauyen Guiwa da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja.
Hakimin mai suna Garba Mohammed ana zarginsa da taimaka wa ’yan bindiga wajen aikata ta’addanci a yankin.
Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a IloriAn kama shi tare da wasu mutum 13 a safiyar ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewar suna hannu wajen taikoman ’yan bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa hakimin yana bai wa ’yan bindiga mafaka a gidansa, inda suke taruwa suna shirya kai hare-haren.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa Aminiya kama hakimin ta wayar tarho.
Ya ce kama mutanen na daga cikin wani samame da ’yan sanda da ’yan sa-kai ke yi domin kawar da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Mashegu.
A ranar 22 ga watan Mayu, 2025, rundunar ta kai samame dazukan Magaman-Daji da kewaye, inda suka fatattaki masu aikata laifi.
A ranar 23 ga watan Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 9 na safe, rundunar ta sake afkawa ƙauyukan Guiwa da Telle bisa sahihan bayanai, inda aka kama hakimin Guiwa, Mallam Garba Mohammed, bisa zargin taimaka wa ’yan bindiga.
An gano babura huɗu da shanu 10 a gidansa, waɗanda ake zargin na ’yan bindiga ne.
Sauran mutum 13 an kama su a sassa daban-daban na Mashegu bisa zargin hannunsu a ta’addanci.
SP Abiodun, ya ce ana gudanar da bincike a kansu domin gano irin rawar da suka taka a ayyukan ta’addanci a yankin.
Ko da yake rundunar ba ta fitar da sunayen waɗanda aka kama ba, wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana sunayen wasu daga cikinsu.
Ya bayyana cewa akwai waɗanda suka fito daga ƙauyukan Wawa a Borgu, Gwajibo, Telle, Dukku a Rijau, Pallagi, Arera, Adogon Mallam da kuma Lumma.
Wani mazaunin New Bussa ya tabbatar wa Aminiya cewa an kama Alhaji Abdullahi Shehu daga Wawa da wasu mutum biyar daga Lumma.
Har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga zargi yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya
Hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya, NRC ta tabbatar da kama ma’aikacinta mai suna Gift Eseeli, mai shekara 38, bisa zargin satar waya a Rafa Yard da ke kan hanyar Warri-Itakpe a harabar tashar jirgin ƙasa (WITS) Jihar Delta.
Jami’an rundunar Man O’war na shiyyar Railway Command ne suka kama ma’aikacin.
A cewar mai magana da yawun hukumar ta NRC, Callistus Unyimadu, binciken farko na nuni da cewa an cire dogayen wayoyin da suke ba da sigina masu sulke mai tsayin 50mm daga na’urorin gefen titin kafin jami’an ‘yan banga ƙarƙashin jagorancin Mista williams Agiake su cafke wanda ake zargin.
2027: ’Yan Najeriya sun yi watsi da takarar Tinubu, sun koka kan tsadar rayuwa Cutar lamoniya ta kama alhazai 99 ’yan ƙasar Indonesiya a SaudiyyaAn gano kayayyakin da aka sace, kuma an miƙa su ga rundunar ’yan sandan Najeriya inda ta fara gudanar da cikakken bincike.
Manajan Darakta na NRC Dakta kayode Opeifa, a cikin sanarwar ya yi Allah wadai da faruwar lamarin tare da jaddada cewa waɗanda aka samu da laifin lalata dukiyar ƙasa za su fuskanci fushin doka.
“Kadarorin titin jirgin ƙasa mallakin kadarorin ƙasar Najeriya ne. Ayyukan ɓarna na barazana ga lafiyar fasinjoji tare da yin zagon ƙasa ga ayyukan muradun sabuwar Najeriya na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
Ya ce, Hukumar ta NRC za ta gurfanar da duk wani mutum ko ƙungiya ciki har da ma’aikatan da aka samu da laifin yin ɓarna ba tare da ƙetare iyaka ba.