‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 5 A Katsina
Published: 25th, May 2025 GMT
Jami’an da aka kashen da suka hada da Kwamandan CWC Mallam Sanusi, rahotanni sun bayyana cewa, suna cikin wani aikin kai dauki ne yayin da wasu ‘yan bindiga kusan ashirin (20) dauke da makamai a babura suka yi musu kwanton bauna a madatsar wani rafi.
A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula ya fitar, maharan wadanda suka boye jikin bishiyar mangwaro, sun kona motar jami’an tsaro kirar Hilux a yayin harin.
Gwamna Radda ya samu rakiyar kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Dr. Nasiru Danmusa; Kwamishinan ’Yansandan Jihar, Daraktan Ma’aikata na Jihar, Shugaban Ma’aikata, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir; da sauran manyan jami’an tsaro.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Shamsudeen Sayaya ne ya jagoranci Radda zuwa inda harin ya faru.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai yayin ziyarar, Gwamna Radda ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin “rashin rashi ga jihar,” sannan ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta kara kaimi wajen tabbatar da tsaron dukkan al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ramuwar Gayya: Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Yawa A Borno
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp