An Gudanar da Zabukan Larduna A Kudancin Kasar Lebanin A Cikin Barazanar HKI
Published: 25th, May 2025 GMT
Mutanen kasar Lebanon sun gudanar da zabubbukan larduna a kudancin kasar a ranar Asabar da ta gabata duk tare da barazanar tsaron da kasar take fama da sun\
Jiragen yakin HKI sun ci gaba da yin luguden boma bomai a kudancin kasar Lebanon duk tare da yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta da suka cimma da kungiyar hizbulla a karshen shekarar da ta gabat.
Kafafen yada labarai sun nakalto mutane suna zabe a garin Jwayya kilomiya 15 kacal kan iyaklar da kasar Falasdinu da aka mamayae. Sunce bas a jin tsoron HKI zata kawo hirik o ba zata kawo ba saboda zabe wajibinsu ne .
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA