Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci A Sama Wa Manoma Masu Renon Tsirrai Rancen Kudi
Published: 24th, May 2025 GMT
“Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi.
Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da Takin Zamni ta Kasa da Kasa (IFDC) da ke kasar nan, Dakta Yusuf Dramani ya bayyana cewa; cibiyar na aiki kafada da kafada da Hukumar NIRSAL, musamman don cike gibin da ake da shi a kasar, wajen samar da rancen kudaden noma ga manoman kasar.
“Duk da cewa, fannin aikin noma na kasar nan, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, amma abin takaici ne ganin yadda ake fuskantar kalubalen rashin samun rancen kudaden noma, musamman a fannin noman renon tsirrai.
“Mun yi amanna da cewa, za a iya sauya wadannan kalubalen da ake fuskanta na samar da rancen kudaden zuwa ga damarmaki, idan har cibiyoyin da ke bayar da rancen kudaden noman sun samar da kayan aikin da suka dace da ilimin da tsare-tsaren da suka kamata da sauransu,” in ji Yusuf.
Ya alakanta gudanar da taron da cewa, abu ne da ya zo kan gaba kuma mai muhimmancin gaske, wanda hakan zai bai wa cibiyoyin da suka halarci taron damar sanin yadda ake gudanar da hada-hadar kasuwanci a fannin na renon tsirrai da kuma irin dimbin damammakin da ke cikin fannin.
Shi kuwa, daraktan gudanar da shirye-shiye na kungiyar ta ‘HortiNigeria’ ta kasa, Mohammed Salasi Idris ya bayyana cewa, manufar da kungiyar ke son cimma, ita ce ta samar da damar samo rancen da ya kai kimanin Yuro miliyan 6, inda ya sanar da cewa, a yanzu mun kai sama da kashi 50 cikin 100 na wannan adadin kudi.
Da yake yin tsokaci kan kalubalen da ake fuskanta a fannin ya sanar da cewa, tsarin samar da rancen kudi na MPR da ke karkashin Babban Bankin Kasa (CBN), ya kara kudin ruwa na bayar da rancen kudin noma daga kashi 18 cikin 100 zuwa kashi 27 cikin 100, inda ya sanar da cewa; wannan babban kalubale ne ga wadanda suke fannin na renon tsirran.
Kazalika, ya sanar da cewa, wani karin kalubalen da manoman da ke Arewacin kasar nan ke fusanta shi ne, na tsadar biyan Leburori.
“Akasarin Leburorinmu, bisa rahotannin da muke samu shi ne, suna zuwa ne daga wasu iyakokin kasar nan, sannan kuma ga yadda darajar Naira ta fadi, inda ya kara da cewa; a cikin shekaru biyu zuwa uku, ba mu ji da dadi ba; musamman ganin yadda darajar Naira ta fadi warwas, kan takardar CFA, wanda hakan ya sa biyan aikin da Leburorin suka yi ya karu”, in ji Idris.
Shi kuwa, a nasa jawabin a wajen taron Jakadan Kasar Netherlands a Nijeriya, Bengt ban Loosdrecht, ya bayyana cewa; fannin na renon tsirrai na taimakawa wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasar da samar da aikin yi tare kuma da samar da abinci mai gina jiki.
Sai dai, Jakadan ya yi nuni da cewa; za a iya samun hakan ne, kawai idan aka samar da rancen kudade ga wadanda suke cikin fannin, wanda ita ce kadai mafita.
Bengt ban Loosdrecht, wanda Mista Folusho Adejoro, Mai Bayar da shawara a bangaren samar da wadataccen abinci da rage dumamar yanayi a ofishin Jakadancin kasar ta Netherlands a Nijeriya ya wakilce shi a wajen taron, ya bayyana cewa, manoma da dama a wannan fannin, na yin aiki tukuru, sai dai, suna fuskantar kalubalen samun rancen kudin renon na tsirrai.
Ya ci gaba da cewa, manufar taron shi ne, domin cike gibin da ake da shi na samar da damar samun rancen kudaden, wanda hakan zai bai wa bankuna da sauran cibiyoyin bayar da rancen kudaden noma fahimtar damar da ke cikin wannan fanni.
Ofishin Jakadanci na kasar ta Netherlands da ke kasar nan ce ke bayar da dauki a shirin habaka renonin tsirrai, wanda aka faro shirin tun a 2021 zuwa 2025, musaman domin tallafa wa fannin tare da samar da wadataccen abinci mai gina jiki a daukacin fadin Nijeriya baki-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: rancen kudaden noma da rancen kudaden ya sanar da cewa samar da rancen ya bayyana cewa renon tsirrai da samar da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Samun Rance Cikin Sauki
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da Kamfanin Bayar da Lamuni a Najeriya (CREDICORP), wani muhimmin shiri a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da nufin rage radadin talauci da bunkasar tattalin arziki ta hanyar fadada hanyoyin samun lamuni.
Da yake jawabi a wani gangamin wayar da kan al’adu a Kano, Shugaban Kamfanin na CREDICORP, Uzoma Nwagba, ya jaddada bukatar sauya ra’ayi game da lamuni, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su dauke shi a matsayin wani makami na bunkasa maimakon akasin haka.
“CREDICORP, wacce aka kafa a karkashin tsarin sabunta fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wata cibiya ce ta kasa da ke aiki don tabbatar da dimokaradiyya ta hanyar samun lamuni ga duk ‘yan Najeriya masu aiki tukuru.
Ya yi nuni da cewa, ta hanyar aikin sa, Kamfanin na baiwa ‘yan Nijeriya damar samun muhimman kayayyaki da ayyuka kamar su hada-hadar motoci, hanyoyin samar da hasken rana, da kayayyakin inganta gida bisa lamuni, maimakon dogaro da iyakacin hada-hadar kudi.
Taron na Kano ya samu wakilai daga gwamnatin jihar, kungiyoyin kasuwa, kungiyoyin kasuwanci, da cibiyoyin hada-hadar kudi, duk sun hada kai a kokarin fadada hanyoyin samar da lamuni na al’adu da rahusa a fadin kasar nan.
Khadija Aliyu