HausaTv:
2025-07-08@21:18:39 GMT

A Yemen An Yi Gangamin Miliyoyin Mutane Na Nuna Goyon Bayan Falasdinawa

Published: 24th, May 2025 GMT

A jiya Juma’a miliyoyin mutane Yemen sun cika dandalin ” Saba’in” dake birnin Sanaa, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu.

An bai wa gangamin taken: ” Muna tare da Gaza” domin jaddada ci gaba da nuna goyon bayan  al’ummar Falasdinu da suke fuskantan kisan kiyashi daga sojojin HKI, da kuma nuna kin amincewa da jefa mutanen yankin cikin yunwa.

Masu gangamin sun yi tir da yadda kasashen larabawa da na musulmi su ka nuna gajiyawa da kuma yin abin kunya saboda yadda su ka yi shiru akan abinda yake faruwa da mutanen Gaza.

Bugu da kari a yayin wannan gangamin an yi jinjina ga sojojin kasar da suke kai wa HKI hare-hare  da kakaba takunkumi akan tasoshin jiragen sama da na ruwa na “Ben Gorio” da kuma ” Haifa”.

Daga cikin wadanda su ka gabatar da jawabi a wurin gangamin da akwai ‘yan Afirka mazauna Yemen, inda su ka yi jinjina ga gagaruwar da Yemen din ke takawa waje taimakawa al’ummar Falasdinu.

Haka nan kuma sun bayyana cewa, batun Falasdinu ya shafi dukkanin musulmi, da masu ‘yanci a duniya baki daya, kuma batu ne na ‘yan adamtaka a matakin farko.”

Bugu da kari sun yi kira ga shugabannin nahiyar Afirka da ma al’ummarta da su kasance a  tare da mutanen Gaza da ake zalunta, su taimake su wajen fuskantar zaluncin da ake yi musu.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Wata bas kirar Macarpollo dauke da mutane da yi hatsari a Jos

Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji  ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato.

Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita.

Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen
  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza
  • Wata bas kirar Macarpollo dauke da mutane da yi hatsari a Jos
  • Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
  • Falasdinawa Kimani 635 Amurka da HKI Suka Kashe A Cibiyoyin Karban Abinci A Gaza
  • Bincike ya nuna ’yan Najeriya ba su gamsu da gwamnatin Tinubu ba
  • Miliyoyin Mutane Sun Yi Juyayin Imam Husain ( a.s) A Karbala
  • Al’ummar A sassan Duniya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa