City ta ba da sanarwa a gabanin fafatawar cewa ta shirya wani babban kyalle mai dauke da sunansa tare da sanya wa wata hanya sunan De Bruyne a makarantar horarwa ta kungiyar, Guardiola yana girmama De Bruyne sosai har ya bayyana dan kasar Belgium din a matsayin dan wasan da ya fi iya kwallo a cikin ‘yan wasan da ya taba horarwa bayan Lionel Messi.

De Bruyne ya fara buga wa City wasa a watan Satumban shekarar 2015, De Bruyne ya buga wasanni 283 a matakin farko, ya ci kwallaye 72 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 119 wanda hakan ya sa ya zama na biyu a jerin wadanda suka fi kowa taimakawa wajen zura kwallo a gasar Firimiya bayan Ryan Giggs da yake da 162.

Wasan da suka yi da Bournemouth shi ne wasa na 142 kuma na karshe da De Bruyne ya buga wa City a gida, inda Dabid Silba mai wasanni 160 ne kadai dan wasan da ya fi shi buga wasannin Manchester City na Firimiya Lig a Etihad.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: De Bruyne ya

এছাড়াও পড়ুন:

Ba Zai Yiwu Amurka Ta Kafawa Chips Kirar Kasar Sin Wani Shinge Ba

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi
  • Mohamed Salah Ya Zama Gwarzon Ɗan Wasan Firimiyar Ingila Na Bana
  • Budurwa ƴar shekara 15 Ta Jefar Da Jariri A Sansanin Ƴan Gudun Hijira A Borno 
  • NNPCL Ta Rufe Matatar Mai Ta Fatakwal
  • El-Rufai Ya Zargi Bangaren Shari’a Da Cin Hanci Da Rashawa
  • GORON JUMA’A
  • Ƴan Ta’adda 13,500 Aka Kashe Cikin Shekaru 2 – NSA Ribadu
  • Ba Zai Yiwu Amurka Ta Kafawa Chips Kirar Kasar Sin Wani Shinge Ba
  • Trump Zai Shirya Liyafar Musamman Ga Manyan Ƴan Crypto