Kamfanonin Sin Da Kazakhstan Na Samun Karin Ci Gaban Hadin Gwiwa A Bangaren Makamashi
Published: 15th, February 2025 GMT
Tawaga ta farko ta ‘yan kasuwan Sin mai kai ziyara ketare da kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ya kafa a sabon shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da muke ciki, ta kai ziyara Kazakhstan, don gaggauta mu’amala tsakanin kamfanonin kasashen biyu da kulla yarjejeniyar hadin gwiwa.
Tawagar ta yi tattaunawa mai zurfi da asusun kasar Kazakhstan na Samruk Kayzana da kungiyar ‘yan kasuwar kasar ta Atamekeh a Astana hedkwatar kasar Kazakhstan, tare da gudanar da taron tattaunawa kan tattalin arziki da ciniki tsakanin ‘yan kasuwar kasashen biyu da kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa 8, wadanda ke shafar bangaren makamashin gas da man fetur da aikin noma da jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa da sauransu.(Amina Xu)
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi
Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara.
Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano, da kuma biyan bashin kuɗin wutar lantarki da man fetur da ake bin hukumar ruwa ta jihar don ci gaba da ayyuka.
Wani ɓangare na kuɗaɗen zai kuma haɗa da biyan basussukan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ke bi, siyan dizal (AGO) da man fetur (PMS) don ayyukan tashoshin tace ruwa, da kuma kula da kayayyakin da tashoshin ke bukata don samar da ruwa tsaftatacce.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA