Hukumar NPA Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci Da Rashawa Da Aka Lakaba Mata
Published: 24th, May 2025 GMT
Onyemekara ya sanar da cewa, rahoton na karya da kafar yada labaran ta wallafa kan zargin cin hancin na biliyoyin Naira, na kanzon Kurege ne, wanda kuma bai da wata tushe, ballantana wata makama.
Kazalika, ya bayar da tabbacin cewa, NPA kamar yadda ta saba, za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa gaskiya da rikon amana, musamman kan abinda ya shafi, ayyukan kashe kudade.
Onyemekara ya kuma yi watsi da batun zargin badakalar hada-hada a ofishin Hukumar NPA da ke a Birtaniya, inda ya sanar da cewa, babu wani batun wata hada-hadar ayyuka a ofishin makamancin haka, da aka gudanar a ofishin.
Ya yi kira ga kafafen yada labarai na kasar nan, da su tabbatar da suna tuntubar Hukumar kan duk wani rahoton da suke son wallafawa, musamman duba da cewa, kofar Hukumar ako da yaushe bude take, domin yin duk wata suka, mai ma’ana.
Ya sanar da cewa, a karkashin Shugabancin Shugaban Hukumar Abubakar Dantsoho, ya mayar da hankali wajen ganin an zamanantar da ayyukan NPA, musamman ta hanyar samar da kayan aiki, da kuma kara gyara sauran kayan da NPA ke amfani da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos
Aƙalla mutane takwas ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Atura Bus Stop, hanyar Lagos-Badagry, lokacin da wata motar haya ƙirar Mazda mai ɗaukar fasinjoji 16 ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota ƙirar DAF. Hukumar LASTMA ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da rashin iya sarrafa mota daga direban motar hayar.
A cikin wata sanarwa, Daraktan Hulɗa da Jama’a na LASTMA, Adebayo Taofiq, ya ce hatsarin ya kasance mai muni matuƙa, inda ya kashe direban motar, yaran moto da sauran fasinjoji shida. Ya ce hatsarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da ɗimuwa. Jami’an LASTMA, da FRSC, da rundunar ƴansanda da Sojoji daga Ibereko sun gudanar da aikin ceto cikin gaggawa.
Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau Jami’in LASTMA Na Bogi Da Ya Sato Mota Ya Shiga HannuAn ceto mutane takwas da suka jikkata, kuma aka garzaya da su Asibitin Gwamnati da ke Badagry don samun kulawar gaggawa. Adebayo ya bayyana cewa hatsarin ya zama darasi, yana mai jaddada cewa gudu, da rashin kiyayewa da sakacin direbobi na ƙara haddasa irin waɗannan hatsarin a tituna.
Babban Manajan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya kai ziyara wurin da hatsarin ya faru, inda ya gargaɗi direbobi su kiyaye gudu da bin dokokin hanya. Ya ce gwamnati ta fara shigar da kayan rage gudu a wuraren da ke da haɗari domin rage yawaitar hatsura. Ya ƙara da cewa dole ne direbobi su nuna kishin ƙasa ta hanyar yin tuƙi cikin hankali da kiyaye lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp