Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar
Published: 24th, May 2025 GMT
Samun Gurbin Shiga Jami’a Da Sauran Manyan Makarantu
Samun damar shiga jami’a a Nijeriya na da matukar wahala a koda-yaushe, sai ga shi wannan shekara ta 2025 ta bullo da wasu sabbin kalubale.
Daga kura-kuren da aka samu yayin yin rajista da kuma gwajin kwamfuta, don rage yawan masu shiga jami’ar, tsarin ragewar na wannan shekarar ya fi na kowace shekara.
Sama da dalibai miliyan 1.9 ne suka rubuta jarrabawar a wannan shekarar, wanda hakan yasa ta zama jarrabawa mafi girma a tarihin hukumar shirya jarrabawar.
Wannan karuwar, ta nuna karuwar yawan al’umma da kuma karuwar bukatar neman ilimi a tsakanin matasan Nijeriya. Har ila yau, wannan na nuni da cewa; adadin guraben da ake da su a jami’o’in kasar nan da sauran manyan makarantu da kwalejojin ilimi, sun yi wa daliban da ake da su kadan.
A halin yanzu, Nijeriya na da sama da jami’o’i 299 da kwalejin fasaha 150 da kuma kwalejojin ilimi da aka amince da su kusan kimanin 205.
Duk da wannan yawa nasu, guraben da aka ware na daukar dalibai, bai wuce tsakanin 500,000 zuwa 700,000 ba a duk shekara, kasa da rabin adadin wadanda suka yi rajistar jarrabawar ta JAMB.
Dalibai da dama, duk kuwa da irin cin da suka yi wa jarrabawar, amma ba su da tabbacin samun guraben shiga jami’ar, wanda hakan a karshe ke haifar da takaici da kuma damuwa.
A shekarun baya, hukumar shirya jarrabawar fagen shiga jami’a (JAMB), ta kayyade maki 140 na jami’o’i, sannan maki 100 a kwalejin fasaha da kwalejojin ilimi. Kazalika, kowace jami’a ko kwaleji akwai kwasa-kwasan da aka fi nema, suka kuma fi bai wa muhimmanci; kamar ilimin koyon likitanci (Medicine), karatun lauya (Law), ilimin Injiniya (Engineering) da kuma na Akanta (Accounting).
Makin da ake kayyadewar, yana canzawa daidai da yadda dalibai suka ci jarrabawar, guraben da ake da su na daukar daliban da kuma kwas din da ake bukata. Don haka, a duk shekarar da aka fi cin jarrabawar, dole ne manyan makarantun su kara yawan adadin makin da suke bukata, sannan kuma idan aka samu akasin haka, nan ma dole ne su sake canja adadin makin.
Haka zalika, ko da dalibi ya samu adadin makin da ake bukata na UTME, akwai yiwuwar kuma ya samu karancin makin da ake bukata na jarrabawar da jami’o’i ke shirya wa dalibai (post-UTME) ko kuma na sakamakon jarrabawar sakandire (O’Lebel).
A bana, tashin hankalin da jama’a suka shiga ya kai makura, sakamakon rahoton da suka samu na faduwa wannan jarrabawa da kuma matsalar da aka fuskanta ta na’ura. Dalibai da dama da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, sun nuna bacin ransu game da abin da suka bayyana a matsayin wani mummunan tsari.
Dangane da wannan abu da ya faru, Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Is-hak Oloyede, ya kafa kwamitin bincike. Bayan bincike na farko, hukumar ta amince da gazawar da aka samu ta fuskar gudanarwa da matsalar na’ura, wanda watakila shi ne musabbabin kawo cikas ga sakamakon jarrabawar daliban da ke Legas da kuma na wadanda ke Kudu-maso-gabas.
A kokarinta na gyara matsalar, Hukumar JAMB ta fara shirin sake jarrabawar daliban da abin ya shafa tare da alkawarin inganta sa ido da kuma gudanar da abin da ya dace.
Kungiyar Dalibai Kasa Ta Shawarci Dalibai Tare Da Bukatar Gyara Hukumar JAMB
Sai dai kuma a wata tattaunawa daban-daban da LEADERSHIP, Shugabannin Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS), sun nuna damuwarsu kan faduwa jarrabawar da daliban suka yi ba bisa laifinsu ba.
Babban Sakatare Janar na Kungiyar (NANS), Anzanku Shadrach ya bayyana cewa, dalilin wannan mummunar faduwa jarrawar da aka samu, sakamakon amfani da na’urorin zamani ne kacokan, kamar yadda ya zargi hukumar shirya jarrabawar ta JAMB da rashin gudanar da kyakkyawan shiri.
Sannan ya kara da cewa, mafi yawancin dalibai ba sa mayar da hankali kan karatunsu, yana mai jaddada cewa; kungiyarsu ta NANS, na gudanar da bincike kan wannan zargi na rashin bin ka’idoji.
A matakin wannan kungiya ta dalibai ta kasa, mun karbi korafe-korafe da dama, amma a banagaren da ake zargi ta fuskar rashin bin ka’idoji, har yanzu ba mu samu wani tabbaci ba. Don haka, mun kafa kwamitin bincike, sannan kuma mun ziyarci Shugaban Hukumar ta JAMB, domin samun bayanan sirri.
“A takaice dai, da zarar rahoton kwamitin ya nuna akwai sakaci cikin al’amarin, za mu bukaci a kori Shugaban Hukumar ta JAMB”, in ji shi.
Har wa yau, jami’in hulda da jama’a na kungiyar dalban ta kasa, Kwamared Samson Ajasa Adeyemi, ya caccaki jadawalin jarrabawar tare da yin kira da a sake duba shi.
Ya ce, sanya karfe 6:30 na safe a matsayin lokacin rubuta jarrabawar, abu ne da ba za a amince da shi ba; musamman idan aka yi la’akari da kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Kazalika, ya bukaci hukumar ta JAMB da ta rungumi fasahar zamani tare da sake zamanantar da harkokikin jarrabawar, yana mai cewa; tsarin da ake da shi yanzu, na da ne wanda bai kamata a ce har yanzu da shi ake amfani ba.
Kalubalen Da Dalibai Suka Fuskanta
A halin da ake ciki yanzu, dalibai da dama sun fito da matsalolin da suka fuskanta yayin gudanar da wannan jarrabawa tare da yin kira wajen gaggauta yin gyara.
Olawanle Timileyin, ya bayyana cewa; tun da fari ya san cewa; wannan sakamako ba nasa ba ne, a lokacin da ya duba.
“Tunda yanzu Hukumar JAMB ta amsa laifinta, ina ganin sake tsara jarrabawar ga wadanda abin ya shafa, ba zai wadatar kadai ba, kamata ya yi hukumar ta bai wa dalibai wasu alawus-alawus, saboda kudaden da suka kashe”, in ji shi.
Wata daliba mai suna Eunice Aegh ta ce, ba a son ranta ta duba sakamakon jarrabawar ba, a cewar tata, ta samu shakku wajen tantance makin da ta samu, bayan samun labarin mummunar faduwar jarrabawar da aka samu.
“Hatta abokaina na makaranta da suka fi ni hazaka, ba su iya samun maki 200 ba,” in ji ta.
Jarrabawar Da Aka Sake Shiryawa
A ranar Juma’ar da ta bgabata ne aka fara gudanar da jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da Hukumar JAMB ta shirya wa wadanda abin ya shafa a dukkanin fadin kasar nan.
Dole ne a sake shirya jarrabawar ga daliban, sakamakon matsalar da aka fuskanta ta na’ura da sauran al’amuran da suka shafi kayan aiki da suka fuskanta yayin rubuta jarrabawar.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, an ga ana sake tantance daliban da za su sake rubuta jarrabawar ranar Juma’ar da ta gabata a cibiyoyi daban-daban, ciki har da Jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a Jihar Anambira.
An kuma samu labarin cewa, wasu daga cikin daliban sun samu sakwanni kasa da sa’o’i 24 na sake shirya jarrabawar, inda da dama suka samu damar tafiya wurare masu nisa da za su rubuta jarrabawar.
Haka zalika, iyayen wadannan dalibai sun bayyana ra’ayoyinsu daban-daban tare da fatan samun nasara wajen rubuta jarrabawar, musamman ganin abin da ya faru na rashin dadi.
Wata uwa mai suna Madam Ijioma Ugwu da ke zaune a Abuja, wadda kuma danta na daya daga cikin wadanda za su sake zana jarrabawar a Jihar Inugu a safiyar ranar Juma’a, ta koka da yadda har yanzu hukumar ta kasa magance wasu matsaloli da ke tasowa.
A cewarta, idan har hukumar ta JAMB za ta ci gaba da kasancewa a matsayinta na hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a, ya kamata ta bunkasa ayyukanta tamkar yadda aka kafa ta a shekarar 1978.
Sannan, ta kuma koka kan yadda aka sanya wa dalibai karfe 6:30 na safe a matsayin lokacin fara rubuta jarrabawar.
Farfesa Yusif Ali Ya Jinjina Wa Oloyede Kan Amincewa Da Kuskuren Da Ya Yi
An yaba wa Shugaban Hukumar JAMB na Kasa, bisa gaskiya da karbar kuskuren da suka yi a fannin da ya shafi na’urar fasaha wajen rubuta jarrabawar wannan shekara ta 2025 a wasu sassan kasar nan.
A wata sanarwa da Farfesan ya fitar, ya yaba da gaskiya da kuma dattakon Oloyede a bangaren jagoranci, wanda kusan za a iya cewa; ba a saba da shi ba, ta yadda ya dauki cikakken alhaki da kuma nuna tausayi ga daliban da abin ya shafa.
Ya lura cewa, Oloyede ya zabi amincewa da laifukan ne maimakon yin watsi da su, kamar yadda yawancin jami’an gwamnati ke yi, kazalika ya bayyana shi a matsayin shugaba nagari, wanda ba ya fifita bukatarsa a kan ta sauran wadanda yake jagoranta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: rubuta jarrabawar Shugaban Hukumar da abin ya shafa Hukumar ta JAMB hukumar ta JAMB wannan shekara jarrabawar da Hukumar JAMB
এছাড়াও পড়ুন:
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Ce; Ba Ta Gaggawar Neman Kulla Alaka Da Kasar Siriya
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta gaggawar kulla alaka da kasar Siriya
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: A halin yanzu babu wata alaka tsakanin Iran da Siriya, kuma Iran ba ta gaggawar kulla alakar. Ya ce: “Lokacin da gwamnatin Siriya ta ga irin yadda alaka da Iran za ta iya taimakawa al’ummar Siriya, a shirye mahukuntan Iran su amsa bukatar ta.”
A wata hira da tashar talabijin ta Al Sharq, Araqchi ya jaddada dimbin damammaki, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran da gaske take yi wajen kulla kyakkyawar huldar makwabtaka da yankin da ke kewaye, kuma Iran ta bi ta wannan hanya.”
Ya kara da cewa: “Iran ta kulla alaka mai kyau ta fuskar siyasa, tattalin arziki da al’adu tare da dukkan makwabtanta da kasashen da ke kewaye, Iran makwabciya ce da Siriya kuma kasashen biyu suna zaune a yanki guda tsawon dubban shekaru.