Hakar man Kolmani: Jihohin Bauchi da Gombe sun gana da NNPC kan bukatun al’umma
Published: 24th, May 2025 GMT
Jami’an gwamnati daga jihohin Gombe da Bauchi sun gudanar da wani taron kwana biyu tare da wakilan kamfanin NNPC da Kamfanin AOML, waɗanda ke gudanar da aikin hakar danyen mai a yankin Kolmani.
An kira taron ne don neman ƙarin bayani kan matakan da AOML ta riga ta ɗauka da kuma gyara kura-kuran da aka gani daidai da Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA), da nufin kauce wasau matsalolin da suka addabi sauran yankuna masu arzikin mai.
Wata sanarwa da Kwamishinan Ma’adinai da Makamashi na Jihar Gombe, Sanusi Ahmed Pindiga, ya fitar, ta ce Kwamitin Haɗin Gwiwa da ke wakiltar jihohin biyu ya gano muhimman fannoni huɗu da ke kawo damuwa, waɗanda suka haɗa da sayen filaye, rashin gudanar da ‘Yancin Aiki (FTO), rashin bin ka’idojin Alhakin Ci Gaban Al’umma (CSR) daga AOML, da kuma gibin sadarwa.
Ya ƙara da cewa don magance matsalolin da aka gano, Kwamitin Haɗin Gwiwa ya yanke shawarar cewa za a kammala sayen filaye da zarar AOML ta samar da takardun biyan kuɗi da suka dace, yayin da NNPC zai ta bi diddigin kamfanin kan biyan kuɗin FTO don hakar mai.
Jami’an Sibil Difens sun bude wuta a garin Jos Za mu gina mayankar dabbobi ta Naira biliyan 3 a Gombe —GwamnatiA cewarsa, za a gudanar da cikakken binciken buƙatu a cikin al’ummomin masu makwabtaka da rijiyar man da waɗanda suka fuskanci matsaloli a sakamakon aikin hakar man don jagorantar shirye-shiryen ayyukan Alhakin Ci Gaban Al’umma (CSR).
Bugu da kari, za a kafa tsarin sadarwa don tabbatar da ingantacciyar mu’amala tsakanin masu gudanar da aikin Filin Mai na Kolmani da dukkan masu ruwa da tsaki.
“Mahalarta taron sun nuna godiya ga shiga tsakani a kan lokaci kuma sun sake jaddada jajircewarsu ta haɗin gwiwa don tabbatar da cewa aikin Filin Mai na Kolmani ya ci gaba ta hanyar da za ta amfani dukkan masu ruwa da tsaki kuma ta bi doka,” in ji Pindiga.
Ya ƙara da cewa: “Sun kuma sake jaddada fatansu cewa burin samun mai da iskar gas na Arewacin ƙasar da aka daɗe ana jira zai tabbata, kuma zai kawo ci gaban tattalin arziki ga yankin.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa
এছাড়াও পড়ুন:
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiYa ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”
Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.
A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.