HausaTv:
2025-07-09@22:59:56 GMT

An Gargadi Shugaban Amurka Dangane Da Fadawa Iran Da Yaki

Published: 25th, May 2025 GMT

Jaridar ;The HIL’ ta kasar Amurka wacce take bada labaran majalisa da siyasar gwamnatin Amurka ta gargadi gwamnatin shugaba Donal Trump kada ta sake irin kuskuren da shugaban kasar Iran Sadam Hussain yaki na fadawa kasar Iran da yaki, tare da tsammanin cewa a cikin yan kwanaki zai ga faduwar jaririyar gwamnatin kasar Iran a lokacin.

Amma sai wankin hula ya kai masa dare, inda ya share shekaru 8 yana fafatawa da mutanen kasar Iran ba kuma tare da samun nasarar ba.

Jaridar ta kara da cewa Iran ba kasace wacce tana dab da faduwa ne sai aje a karasa faduwarta ba. Kasashen wacce kan mutanen kasar a hade yake a duk lokacinda na waje yayi kokarin mamayar kasar.

Labarin ya kara da cewa, jaridar ta bukaci gwamnatin Trump kada ta sake kuskuren da sadan Hussain yayi kuma ta kasar ta laluma ta hanyar diblomasiyya, don warware dukkan matsalolin da ke tsakaninsu da ita.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12

Ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake halattan taron kungiyar raya tattalin arziki ta Bricks ya yabawa kungiyar kan yin tir da Amurka da kuma HKI kan keta hurumin kasar da yaki na kwanaki 12 da kuma da kuma kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar ta zaman lafiya wadanda suke Fordo Natanz ta kuma Esfahan.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalti ministan yana fadar haka a taron kungiyar karo 17 wanda ke gudana a hilin yanzu a birnin Rio De jenero na kasar Brazil.

A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne jiragen yaki na HKI suka kutsa cikin Iran inda suka kashe manya-manyan kwamandocin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliyar kasar ga shahada.

Bayan haka sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan tashar talabijin ta “Khabar” na harshen farisanci a hukumar tashoshin radio da talabijin na kasar.

Banda haka jiragen yakin Amurka B-2 sun kai hare0hare kan cibiyoyin Nukliyar kasar guda ukku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso
  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliya Kasar Idan Tanaso
  • Hizbullah Ta Kasar Lebanon Ta Godewa JMI Dangane Da Tallafawa Kungiyar Saboda Gwagwarmaya Da HKI
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce; An Rusa Hanyar Tattaunawa da Iran Kan Shirin Na Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
  • HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12
  • Sheikh Ibrahim Zakzaky Ya Taya JMI Murnar Nasara A Kan Mikiyanta
  • Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato