Don haka, CHINADA tana nuna matukar adawarta ga duk wani yunkuri na bayyana shan kwayoyi masu kara kuzari a matsayin wai ci gaban kimiyya, tare da yin kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a harkar wasanni na duniya da su tashi tsaye, su hada kai wajen yin fatali da wasannin da aka amince a sha kwayoyin kara kuzari.

(Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta naɗa Luciano Spalletti a matsayin sabon kociya bayan sallamar Igor Tudor da ta yi a farkon makon nan.

Juventus ta ƙulla yarjejeniya da tsohon kociyan na Inter Milan da Roma da Udinese da Zenit St Petersburg da kuma tawagar ƙasar Italiya, har zuwa ƙarshen wannan kakar, yayin da take fatan samu gurbin zuwa gasar Kofin Zakarun Turai ta Champions League ta baɗi.

Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum

Spalletti, shi ne kociyan da ya jagoranci Napoli wajen lashe gasar Serie A a 2023, wadda ita ce karon farko cikin shekaru 33, inda a yanzu ake fatan zai ƙara daidaita Juventus da ke fama da rashin katabus da matsalolin kuɗi tun daga 2022.

Spalletti, wanda aka sani da ƙwarewa wajen gina ƙungiya mai ƙarfi, ya dawo horaswa bayan gazawar da ya yi a matsayin kociyan Italiya a gasar Euro 2024, da kuma shan kashi a hannun Norway yayin wasan farko na neman tikitin Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Zuwa yanzu dai Juventus tana matsayi na bakwai a gasar Serie A da tazarar maki shida tsakaninta da Napoli da ke saman tebur, inda wasan farko da Spalletti mai shekaru 66 zai ja ragama shi ne da Cremonese.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari
  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
  • Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan