Ya Kubuta A Hannun ‘Yan Bindiga Bayan shafe Kwanaki 8 Yana Gudu A Dajin Sokoto Da Neja
Published: 25th, May 2025 GMT
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya ce an yi garkuwa da Ilya ne daga kauyen Gatawa tare da mahaifinsa.
Iliya da mahaifinsa dukkansu daga karamar hukumar Sabon-Birni ta jihar Sokoto. An yi garkuwa da su ne a cikin watan Afrilu, yayin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyensu, suna ta harbe-harbe, inda daga nan ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Ilya ya bayyanawa ‘yansanda cewa, ya tsere daga sansanin ‘yan bindigar ne bayan ya yi ta gudu a dajin har na tsawon kwanaki takwas sannan ya hadu da jami’an ‘yansanda a jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense
Wannan nasarar ta sa Chelsea ta ƙara samun kuɗi fam miliyan 22 wanda ya ƙaru kan fam miliyan 60 da suka riga suka samu a gasar.
Hakan yana nuna cewa suna samun riba daga siyan Joao Pedro da suka yi a fam miliyan 55.
Fluminense ta nuna rashin jin daɗi lokacin da alƙalin wasa ya soke bugun daga kai sai gola da aka ba su, bayan duba na’urar VAR.
Amma Chelsea na fuskantar damuwa da yiwuwar raunin ɗan wasan tsakiya Moises Caicedo ya samu.
Chelsea za ta kara da Real Madrid ko Paris Saint-Germain a wasan ƙarshe a ranar Lahadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp