Ofishin watsa labaru na hukuma a Gaza ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyin jin kai, da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu na doka da kyawawan halaye, su tsoma baki domin ceto da fararen hula a Gaza.

Ofishin watsa labarun na hukuma a Gaza ya  kuma yi kira da a tseratar da mutanen na Gaza daga yunuwar da suke fuskanta, ta hanyar yin matsin lamba da a bude hanyoyin shigar da kayan taimako da agaji cikin yankin.

Ita kuwa hukumar lafiya ta yanki ta sanar da yadda sojojin na HKI suke ci gaba da kai hare-hare akan  asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya da hakan ya sabawa dokokin yaki.

Ofishin watsa labaru na hukumar Gaza ya kuma sanar da cewa; Har yanzu yankin yana fama da matsanancin killace shi da aka yi, da hana shigar da kayan agaji.

Daga lokacin sake komawa yaki na bayan nan da HKI ta yi, tun kwanaki 80 da su ka gabata,mutane 58 sun rasa rayukansu saboda rashin abinci mai gina jiki, sai kuma wasu 242 da yunuwa da rashin magani su ka kashe,mafi yawancinsu wadanda su ka mayanta.  Haka nan kuma wasu mata masu ciki fiye da 300 su ke cikin nasu ya zube saboda rashin abinci mai gina jiki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Tabarbarewar Tsaro Ta Kara Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta

Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa.

Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa.

‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo.

Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa maso Gabas, cikin matsanancin rikici, rashin kyakkyawan shugabanci, wadanda rashin sanya hannun jari ke yanke jin dadin rayuwarsu.

Al’amarin wadannan yaran bai tsaya kadai kididdiga ba. Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da abin da ba a yi tsammani ba: Nijeriya ce ta fi kowacce kasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya. Idan ka tara uku za ka samu daya daga cikinsu ba ya zuwa makaranta, wato ba ya samun ilimin boko a halin yanzu.

“Wannan matsalar ba ta tsaya kadai ga ilimi ba, al’amari ne dake bukatar taimakon gaggawaa kasa.

Idan ba a dauki matakin gaggawa ba, Nijeriya na fuskantar afkawa hadarin kasa yin kafada da sa’anninta, wajen ci gaba sace jama’a da rashin kyakkyawar gami da kakaba wa jama’a talauci, tsatsauran ra’ayi, da rashin zaman lafiya.”

A cewar wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Ahmed Idris, matsalar ilimi a Nijeriya na kara ta’azzara, musamman a yankunan da ke da karancin makarantu.

Ya ce yara da yawa har yanzu suna tafiya mai nisa zuwa makaranta, idan kuma sun halarci makarantar za ka samu babu kwararrun malamai.

Wani lokaci kuma, ana samun karancin ingancin malamai.

“Rashin ingancin koyarwa ya sa dalibai ba za su iya karatu ko yin lissafi ba bayan sun shafe shekaru a makaranta, don magance wannan, dole ne gwamnati ta ba da fifiko ga Ilimi kyauta da yin amfani da fasaha don cike gibin.

Ilimi shi ne ginshikin rage talauci, aikata laifuka, da rashin aikin yi, gina hanyoyin koyar da sana’o’i da kuma samar wa ‘yan Nijeriya makoma nan gaba,” in ji shi.

Wani malami da ke zaune a Abuja, Peter Ojo, ya yi gargadin cewa Nijeriya ba za ta iya kaucewa barazanar da ke kunno kai wacce ‘yan zamani marasa ilimi ke yi ba.

A cewarsa, dangantakar ilimi da ci gaban tattalin arziki ba abu ne da za a iya musantawa ba.

Ya ce, “Ta hanyar ba da fifiko ga ilimi, kasar za ta iya canza matasanta zuwa ga samar da canji mai kyau da ci gaban kasa. Bayan haka, magance duk wata matsala ta zamantakewa ta dogon lokaci dole ne sai an bi ta hanyar ilimi.”

Ya kuma kara bayyana yadda ake fama da karancin kudade a fannin ilimi, inda kashi 7.3 cikin 100 ne kawai na kasafin kudin kasar da aka ware wa ilimi, wanda bai kai kashi 15-20 bisa 100 da hukumar UNESCO ta ba da shawarar ba.

Ya ce rashin kudi a matsayin wani muhimmin al’amari da ke taimaka wa gurbacewar ababen more rayuwa, cunkoson ajujuwa, da rashin isassun kayan koyarwa, rashin wadatar dalibai da malamai da karancin ababen more rayuwa a makarantu duk su ke haifar da wadannan matsaloli.

Sai dai ya amince da ci gaban da wasu jihohin Nijeriya suka samu a baya-bayan nan, kamar su Enugu, Jigawa, Kano, da Kaduna, wadanda suka ware sama da kashi 26 na kasafin kudinsu ga ilimi a shekarar 2025.

A ‘yan kwanakin nan, gwamnatin tarayya da na jihohi da wasu kamfanoni masu zaman kansu na kokarin ganin an shawo kan matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya. A kwanakin baya, babbar sakatariyar hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC), Aisha Garba, ta ce hukumar za ta fadada rajista da shigar da su cikin tsarin ilimin boko domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar nan, musamman a yankunan karkara.

Ta kuma bayyana cewa galibin yaran da ba sa zuwa makaranta suna zaune ne a yankunan karkara kuma aksarinsu ‘ya’yan talakawa ne, inda rashin daidaiton tattalin arziki ke haifar da fatara a gidaje da dama.

Ta kuma jaddada bukatar kara bayar da shawarwari don magance muhimman kalubalen ilimi a Nijeriya.

Har ila yau, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna ‘Lumina Programme’, na magance yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

Karamar ministar ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad Ahmad, ta bayyana cewa shirin zai samar da ilmin karance-karance da kuma ilmin lissafi, musamman ga yara mata a cikin al’ummomin da ke da wuyar isar da sako.

A Kaduna, gwamnatin jihar ta ce za ta horas da mambobin kwamitin kula da makarantu (SBMC) 8,700 domin inganta ilimi a matakin farko a jihar.

Mukaddashin shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB) Mubarak Muhammad ne ya bayyana hakan a Kaduna kwanan nan.

Har ila yau, wata kungiya mai zaman kanta (NGO) mai suna IA-Foundation, ta tara Naira miliyan 30 a taron agajin da ta gudanar kwanan nan a birnin Landan domin tallafa wa ilimin yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

Shugabar kungiyar ta IA-Foundation, Misis Ibironke Adeagbo, ta ce za a tura asusun ne domin taimakawa muhimman ayyukan kungiyar kai tsaye.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF
  • Rashin abinci mai gina jiki a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane 299
  • An fara aikin gina mayankar dabbobi ta Naira biliyan 3 a Gombe
  • Gyaran Jiki Da Kyawun Fata
  • Hukumar NPA Ta Yi Watsi Da Zargin Cin Hanci Da Rashawa Da Aka Lakaba Mata
  • Yadda Tabarbarewar Tsaro Ta Kara Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta
  •  Fiye Da  Falasdinawa 50 Ne Su Ka Yi Shahada A Yau Alhamis
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kashe Naira Tiriliyan 1.5 Don Magance Matsalar Abinci — Minista
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Nasarorin Noma da Tsaron Abinci Karkashin Shirin Renewed Hope