Nijeriya Na Da Karfin Tattalin Arzikin Sarrafa Kayan Dandanon Da Muke Bukata A Cikin Gida – Yahaya Yakubu
Published: 24th, May 2025 GMT
Na yi imanin za mu iya hakan
Kuma muna fasahar da za mu iya aiwatar da hakan?
Idan aka yi la’akari da albarkatun noma da Nijeriya ke da shi, musamman a cikin amfanin gona irin su rogo da rake, da kuma ta hanyar saka hannun jari kan ababen more rayuwa da fasahar kere-kere, akwai gagarumin yuwuwar bunkasa damar samar da MSG na cikin gida ta hanyar amfani da wadannan albarkatun kasa da ake samu.
Muna da injiniyoyi da yawa wadanda za su iya gyara injinan. Muna da dukkan abubuwan da ake bukata a Nijeriya don samar da kayan dandano. Yawanci muna samun abubuwan da duk da muke bukata. Idan kana bukatar ruwa mai yawa, muna da madatsun ruwa a Shiroro, Kaduna da Neja. Muna da filaye da yawa wadanda za su iya zama na noman rake. Idan ka je Adamawa, ana shuka rake.
Yawancin jihohin Arewa suna shuka rake kuma ana samun amfani da ingantacciyar. Tare da dabarun saka hannun jari da ci gaba, Nijeriya na da damar kafa nata wuraren samar da MSG, tare da yin amfani da albarkatu masu yawa na noma. Muna da karfin yin hakan.
An samu sabanin ra’ayi game da MSG a Nijeriya, wane hali ake ciki yanzu?
Tun kafin yanzu, ana samun hasashe marasa dadi. Amma sannu a hankali al’amura sun fara yin kyau. A halin yanzu, hasashe, da alama hasashen yana canzawa sannu a hankali, kuma mun fara ganinsa saboda karuwar sha’awar masu amfanin da abin.
Wace rawa kayanku ke taka wajen tallafa wa kasuwancin gida da ’yan kasuwa?
Cibiyarmu na raba kaya a fadin Nijeriya. Mun samar da tsarin a kamfanin domin raba kayayyaki wanda zai bai wa ‘yan kasuwar Nijeriya damar farawa da bunkasa kasuwancinsu. Ta hanyar ba da dama da rarraba samfuranmu a duk fadin kasar, ta hanyar ba da horo, da tallafin tallan da muke bayarwa, muna karfafa wa dillalai da kananan ‘yan kasuwa masu samar da kudin shiga da daukar wasu a cikin al’ummominsu.
Ta yaya kayayyakinku ke karfafa kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs) ta hanyar sadarwa da rarraba ta?
Kamfaninmu yana hadin gwiwa tare da kanana da matsakaitan masana’antu (SMEs), kirkirar dama ga kasuwancin gida don bunkasa. Daga masu ba da kaya zuwa masu ba da ayyuka, ayyukanmu suna habaka kasuwanci, suna tallafa wa kirkirar ayyuka.
Ta wace hanya ce kayanku ke ba da gudunmawa ga abinci masu gina jiki?
Muna taka muhimmiyar rawa wajen habaka ilimantarwa, kwarewa, da ayyuka a cikin sassan kayan abinci masu gina jiki na Nijeriya, ta hanyar shirye-shiryenmu na koyar da abinci mai gina jiki da hadin gwiwar kwararrun masana kiwon lafiya. Ta hanyar yin hulda tare da al’ummomin likitoci da kimiyya, AJINOMOTO yana shirya tarurrukan karawa juna sani da bita don tattauna aminci da fa’idodin kayan abinci.
Ta yaya wannan alama ke tallafa wa samar da abinci da ilimin abinci mai gina jiki a Nijeriya?
AJINOMOTO yana ba da gudummawa sosai ga ingancin abinci da ilimin abinci mai gina jiki a Nijeriya ta hanyar tabbatar da amincin samfura da inganci, wannan shi ne muna ba da tabbacin mafi kyawun masana’antu da ayyukan samarwa. Har ila yau, ta hanyar ba da shawara don rage gishiri, mun gane abubuwan da ke tattare da lafiyar jiki mai yawa na sodium; don haka AJI-NO-MOTO® ya zama madadin mafi koshin lafiya ga gishirin gargajiya.
Za ka iya ba da tarihin wannan kamfani?
AJINOMOTO GROUP shi ne ya samar da AJI-NO-MOTO®, kayan dandano na umami na farko a duniya, wanda ya wanzu tun 1909, wato, sama da shekaru 100.
Mun himmatu wajen ba da gudummawa ga jin dadin dan’Adam, jin dadin rayuwar al’umma da jin dadin duniya tare da “Kimiyyar Amino”. An fara samar da AJI-NO-MOTO® a Nijeriya a shekarar 1991 tare da kafa kamfanin Ajinomoto Foods Nigeria Limited (AFN) wanda ya fara Sayar da Kayayyakin dandano na AJI-NO-MOTO® Umami a kasar tare da masana’antar shiryar kaya a Legas.
A yau, kamfanin ya fadada samfuran samfuransa daga MSG (monosodium glutamate), mashahurin AJI-NO-MOTO® zuwa kayan dandanon MaDish® da DeliDawa™. Kuma yanzu muna ci gaba da wasu samfurori. Don haka, kamfani ne da ke da kayayyaki iri-iri da ake nufi don biyan bukatun ’yan Nijeriya.
Wane irin kaso kasuwarku ke samu a masana’antar abinci ta Nijeriya?
Kasuwar Nijeriya wata kasuwa ce mai karfin gaske, wacce mutane ke da zabi daban-daban dangane da kayan dandano. Duk da rikitarwa,
Zan iya fayyace cewa muna sarrafa babban kaso na kasuwa a rukunin da muke taka rawa. Alamar yana da ginshiki mai karfi, kuma ya girma sosai a cikin kasuwar. Baya ga haka, muna da kayayyaki masu inganci. A halin yanzu, muna rike sama da kashi 70 na kasuwancin MSG a Nijeriya. Mantra na kamfani namu “Ku Ci Lafiya, Ku rayu lafiya” yana karfafa sadaukarwarmu don taimaka wa mutane su gina lafiya. Fiye da kowane lokaci, ko yaushe muna himmantuwa ga jin dadin rayuwar mutane, al’umma da duniya.
Ka yi magana game da bangaren kasuwanci, yaya game da masu amfani da kayan?
A cikin sanin yanayin masu amfani da shi, mun dage kan kirkira, sadaukar da kai ga ingancin samfuran, masu tsafta kuma hakan na ba mu damar yin gasa.
Mun ware samfura da muka mai da hankali kan kirkirar su da suka dace da al’adun dafa abinci na Nijeriya. Misali shi ne ci gaban DeliDawa™, kayan dandanon da aka shirya shi ta hanyar daddawar gargajiya. Wannan samfurin yana ba da dandanon gida. Muna daya daga cikin kananan kamfanoni a cikin nau’ikan kayan aikin da aka ba da cikakken tabbaci daga hukumar kula da tsaftar abinci kamar NAFDAC da SON.
Wadanne matakai ne kamfaninku ya bi don sauke wannan ilimi zuwa ga masu amfani, wajen ƙara ilmantar da su dangane da ayyukan CSR?
Muna da hadin gwiwar kungiyoyi da yawa, ciki har da gwamnati, tallafin kiwon lafiya, kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin ilimi da sauransu don fitar da ayyukan mu na CSR. Muna ilmantar da mutane ko dai ta hanyar hadin kai ko daukar nauyin aiki. A cikin ‘yan kwanakin nan, mun samar da ayyuka a fannin kiwon lafiya, ilimi, karfafa wa mata, tabbatar da tsaftar muhalli da dai sauransu.
Ta yaya kuke amfani da fasaha don tabbatar da samun samfurori masu inganci?
Muna mai da hankali kan bambance samfuranmu ta hanyar ba da sabbin abubwa mafi inganci. Wannan ya hada fasahar ci-gaba ko wasu fannoni na musamman wadanda suka tare da mu.
Idan kuna magana game da fasaha, wannan ci gaba ne na yau da kullum. Kowane lokaci muna hadin gwiwa don habaka ingantaccen aiki da ingancin samfuri, don haka muna ba da gudummawa ga daidaiton samfura. Misali, a farko, muna amfani da wasu injina wadanda ke da layika da suka samar da kayayyki nau’u biyu kawai. Mun kuma fadada shi zuwa kusan inji mai layi shida daidai da ka’idojin duniya.
Wane adadi kuke samarwa a duk shekara?
Saboda manufofin kamfani game da sirri, ba zan iya bayyana takamaiman alkaluman samar da kayayyaki ba, amma dai zan iya tabbatar maka cewa karfinmu ya yi daidai da bukatun kasuwa da hasashen ci gaba.”
Da yake ana magana ce game da yuwuwar DeliDawa, shin a zuciyarku kun taba tunanin fitar da wasu samfuran zuwa kasashe makwabta?
Bisa la’akari da yuwuwar ci gaban da ake samu a yankin kudu da hamadar sahara, tabbas muna da wani mutum da ke gudanar da harkokin kasuwanci zuwa kasashen waje. Kuma ta hanyarsa kadai, mun gabatar da DeliDawa™ da aka kai wasu kasashen Afirka kamar Guinea, Cote d’Iboire da Ghana. DeliDawa™ yana habaka bayanan dandano na asali daban-daban. Yanzu, yawancin wadannan kasashe sun zama babbar kasuwar kayan dandano. Ba abu mai sauki ba amma mun sami ci gaba. Kamar yadda ka sani, ba shi da sauki a fara sabon abu kuma ka girma cikin dan gajeren lokaci.
AJINOMOTO zai ci gaba da jajircewa wajen samar da samfura ta hanyar sadarwa mai yawa don karfafa kasancewarsu a kasuwannin Afirka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya Ta hanyar ba da ta hanyar ba da kayan dandano da kayayyaki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci A Sama Wa Manoma Masu Renon Tsirrai Rancen Kudi
“Fanin na kuma taimaka wa wajen samar da ayyukan yi da samar da abinci mai gina jikin Dan’adam da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, musamman duba da wayar da kai da ake yi na samar da abinci mai gina jiki,“ in ji shi.
Shi ma, a nasa jawabin a wajen taron, Daraktan Cibiyar Bunkasa Samar da Takin Zamni ta Kasa da Kasa (IFDC) da ke kasar nan, Dakta Yusuf Dramani ya bayyana cewa; cibiyar na aiki kafada da kafada da Hukumar NIRSAL, musamman don cike gibin da ake da shi a kasar, wajen samar da rancen kudaden noma ga manoman kasar.
“Duk da cewa, fannin aikin noma na kasar nan, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen kara bunkasa fannin tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, amma abin takaici ne ganin yadda ake fuskantar kalubalen rashin samun rancen kudaden noma, musamman a fannin noman renon tsirrai.
“Mun yi amanna da cewa, za a iya sauya wadannan kalubalen da ake fuskanta na samar da rancen kudaden zuwa ga damarmaki, idan har cibiyoyin da ke bayar da rancen kudaden noman sun samar da kayan aikin da suka dace da ilimin da tsare-tsaren da suka kamata da sauransu,” in ji Yusuf.
Ya alakanta gudanar da taron da cewa, abu ne da ya zo kan gaba kuma mai muhimmancin gaske, wanda hakan zai bai wa cibiyoyin da suka halarci taron damar sanin yadda ake gudanar da hada-hadar kasuwanci a fannin na renon tsirrai da kuma irin dimbin damammakin da ke cikin fannin.
Shi kuwa, daraktan gudanar da shirye-shiye na kungiyar ta ‘HortiNigeria’ ta kasa, Mohammed Salasi Idris ya bayyana cewa, manufar da kungiyar ke son cimma, ita ce ta samar da damar samo rancen da ya kai kimanin Yuro miliyan 6, inda ya sanar da cewa, a yanzu mun kai sama da kashi 50 cikin 100 na wannan adadin kudi.
Da yake yin tsokaci kan kalubalen da ake fuskanta a fannin ya sanar da cewa, tsarin samar da rancen kudi na MPR da ke karkashin Babban Bankin Kasa (CBN), ya kara kudin ruwa na bayar da rancen kudin noma daga kashi 18 cikin 100 zuwa kashi 27 cikin 100, inda ya sanar da cewa; wannan babban kalubale ne ga wadanda suke fannin na renon tsirran.
Kazalika, ya sanar da cewa, wani karin kalubalen da manoman da ke Arewacin kasar nan ke fusanta shi ne, na tsadar biyan Leburori.
“Akasarin Leburorinmu, bisa rahotannin da muke samu shi ne, suna zuwa ne daga wasu iyakokin kasar nan, sannan kuma ga yadda darajar Naira ta fadi, inda ya kara da cewa; a cikin shekaru biyu zuwa uku, ba mu ji da dadi ba; musamman ganin yadda darajar Naira ta fadi warwas, kan takardar CFA, wanda hakan ya sa biyan aikin da Leburorin suka yi ya karu”, in ji Idris.
Shi kuwa, a nasa jawabin a wajen taron Jakadan Kasar Netherlands a Nijeriya, Bengt ban Loosdrecht, ya bayyana cewa; fannin na renon tsirrai na taimakawa wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasar da samar da aikin yi tare kuma da samar da abinci mai gina jiki.
Sai dai, Jakadan ya yi nuni da cewa; za a iya samun hakan ne, kawai idan aka samar da rancen kudade ga wadanda suke cikin fannin, wanda ita ce kadai mafita.
Bengt ban Loosdrecht, wanda Mista Folusho Adejoro, Mai Bayar da shawara a bangaren samar da wadataccen abinci da rage dumamar yanayi a ofishin Jakadancin kasar ta Netherlands a Nijeriya ya wakilce shi a wajen taron, ya bayyana cewa, manoma da dama a wannan fannin, na yin aiki tukuru, sai dai, suna fuskantar kalubalen samun rancen kudin renon na tsirrai.
Ya ci gaba da cewa, manufar taron shi ne, domin cike gibin da ake da shi na samar da damar samun rancen kudaden, wanda hakan zai bai wa bankuna da sauran cibiyoyin bayar da rancen kudaden noma fahimtar damar da ke cikin wannan fanni.
Ofishin Jakadanci na kasar ta Netherlands da ke kasar nan ce ke bayar da dauki a shirin habaka renonin tsirrai, wanda aka faro shirin tun a 2021 zuwa 2025, musaman domin tallafa wa fannin tare da samar da wadataccen abinci mai gina jiki a daukacin fadin Nijeriya baki-daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp