Gasar Wasanni Ta Kasa: Jihar Binuwai Ta Samu Kyaututtuka 9 Zuwa Yanzu
Published: 25th, May 2025 GMT
George Iniobong ɗan shekara ashirin da biyu daga tawagar Jihar Binuwai ya samu kyautar azurfa a gasar maza ta Judo mai nauyin kilo 60 a yau Lahadi, yayinda ake cigaba da gasar wasanni ta ƙasa karo na 22 (NSF) da ke gudana a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Nasarar da George ya samu ya sa tawagar ta Jihar Binuwai ta samu kyautukan tagulla da Azurfa 9 jimilla a gasar, wakilinmu ya ruwaito cewa, Iniobong, ya yi matuƙar taka rawar gani a wasan inda ya samu nasara a kan abokin karawarshi daga jihar Ogun cikin mintunan ƙarshe na karawar.
George Iniobong yayinda yake zantawa da manema labarai bayan samun wannan gagarumar nasarar, ya yaba wa Gwamnan Jihar Binuwai, Fr. Hyacinth Alia domin abinda ya kira gudunmawar da gwamnan ya ba shi da sauran ‘yan wasa daga jihar domin su nuna bajintarsu a wasannin na Gateway wanda ya haɗa ‘yan wasa daga dukkan jihohin kasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja, domin fafatawa a wasanni daban-daban, da niyyar inganta hadin kai da kwazo a fadin Najeriya.
“Duk da cewar nayi tunanin samun kyautar zinare a wannan wasan amma ina sa ran kasancewa cikin masu samun wannan kyautar zuwa gaba, Nasara ta na tare dani da kuma jihar Binuwai” inji shi, “Duk da haka na ƙara samun ƙwarin gwuiwa da gogewa, kuma a shirye nake in bayar da duk abin da zan yi wajen samun nasarar jihar idan wata dama ta samu ya kara da cewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Jihar Binuwai jihar Binuwai
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA