Ukraine Da Rasha Sun Yi Musayar Fursinoni Tsakaninsu Irinsa A Karon Farko
Published: 25th, May 2025 GMT
A jiya Asabar ce kasashen Rasha da Ukraine suka yi musayar Fursinoni a tsakanin, karon farko irinsa tun bayan fara yaki a tsakaninsu fiye da shekaru 3 da suka gabata.
Shafin yanar gizo na Labarai Arabs News ya bayyana cewa an yi musayar furisnonin ne a jiya Asabar kuma ko wace kasa ta sake fursinonin yaki har 390.
Labarin ya kara da cewa a dai dai lokacinda aka yi musayar fursinonin sojojin Rasha sun yi loguden wuta a kan birnin Kiyev babban birnin kasar ta Ukraine.
Majiyar gwamnatin kasar Ukraine ta bada sanarwan cewa akalla mutane 10 sun ji rauni saboda luguden watan.
A makon da ya gabata ne kasashen biyu suka tattauna a tsakaninsu a birnin Istambul na kasar Turkiyya, inda ake saran zasu tsagaita budewa juna wuta amma hakan bai faru ba saboda sabanin da ke tsakanin kasashen biyu. Amma duk da haka sun amince su yi musayar fursinoni a tsakaninsu wanda ya tabbata a jiya. Ana saran kasashen biyu zasu sake haduwa nan kusa a kokarin tsagaita wuta a tsakaninsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
A zantawar Sule Lamido da BBC, ya bayyana cewa; an yi masa kora da hali a hedikwatar jam’iyyar ta PDP.
Ya kara da cewa, ya je hedikwatar jam’iyyar PDP ne; domin karbar fom na takarar shugabancin PDP, sai ya samu ofishin da ya kamata ya karba a kulle, da ya tambaya sai aka ce da shi, a hannun gwamnan Adamawa kadai zai samu fom din.
Lamido ya ci gaba da cewa, ba ya fata a kai ga matakin da za a hana shi shiga takarar, “domin ina tunanin rigimar cikin gida ce, sannan kuma za mu iya samun maslaha a cikin gidan. Amma idan hakan bai yiwu ba, daga nan kuma na san me zan yi,” in ji shi.
Haka zalika, Sule Lamido ya ce; a shirye yake ya tsaya takarar shugabancin jam’iyyar a zaben da za a yi lokacin babban taron jam’iyyar a watan Nuwamban wannan shekara a birnin Ibadan na Jihar Oyo.
Bugu da kari, Lamidon ya sha alwashin tafiya kotu idan har aka ki sayar masa da fom din tsayawa takarar.
Kazalika, rahotanni sun tabbatar da cewa; tuni tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki ya yanki nasa fom din, a daidai lokacin da aka ki sayar wa da tsohon gwamnan na Jigawa fom din takarar shugabancin jam’iyyar ta hamayya, wato PDP.
Har wa yau, Jam’iyyar PDP ta sanar da dage tantance dan takara daga ranar Talata zuwa wani lokaci nan gaba, duk da cewa; jam’iyyar ba ta fadi dalilin yin hakan ba.
Haka nan, sanar da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin dantakarar maslaha daga Arewacin Nijeriya ya bar baya da kura, inda wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yammacin kasar, shiyyar da Turaki ya fito suka yi watsi da matakin da gwamnoni suka dauka.
Kazalika, shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Sakkwato, Muhammad Bello Aliyu na cikin shugabannin da suka yi fatali da matakin da gwamnonin suka dauka, saboda a cewarsa, ba a ba su damar zama su tattauna ba, gabannin tsayar da Turakin. Kana kuma, an sake samun wasu jiga-jigan jam’iyyar daga Jihar Kebbi da suka yi fatali da wannan maslahar.
Dangane da wanan sabuwar rigima ko rikici, malami a kwalejin ilimi ta share fagen shiga jami’a da ke Kano kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Dakta Kabiru Sa’id Sufi ya ce; ana neman fama karaya ne a yunkurin gyara targade.
“Mun dauka cewa, tunda aka zo batun zaben shugabanci, matsalolin da jam’iyyar ke ciki sun kusa zuwa karse, musammman ganin har an yi kokarin rarraba mukamai zuwa shiyya-shiyya, amma kuma sai hakan ya bar baya da kura.
“Yanzu haka, an fara samun korafi daga bangarori da dama, ciki har da daga wadanda ake ganin ba su da wata matsala.”
Haka nan, ya kara da ce; hana Sule Lamido sayen fom din takarar shugabancin jam’iyyar, wani babban al’amari ne, domin kuwa a cewar tasa; hakan ya kara haifar da rashin gamsuwa a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.
Ya ce, “Akwai da ma wasu da suke ganin an lasa musu zuma a baki a Arewacin kasar na tsayawa takara, sai daga baya suka gane cewa, ba da gaske ake ba. Idan aka duba, za a ga akwai rashin gamsuwa daga bangarori da yawa. Ko bangaren Shekarau ma, sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al’amuran.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA