Masana’antar Samar Da Injuna Ta Kasar Sin Ta Samu Tagomashi A 2024
Published: 14th, February 2025 GMT
Kungiyar masu sana’ar samar da manyan injuna ta kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, masana’antar ta samu ci gaba mai inganci a shekarar 2024, biyo bayan shirin kasar na daukaka ingancin manyan injuna da ma dabarun raya masana’antar da aka dauka.
A shekarar 2024, ribar da manyan kamfanonin samar da manyan injuna suka samu ya karu kan na 2023 da kaso 6 cikin dari.
A bara, na’urorin samar da lantarki daga iska ne suka mamaye fiye da rabin kayayyakin samar da lantarki a kasar.
A shekarar 2024, cinikin motoci masu amfani da makamashi mai tsafta ne ya dauki kaso 40.9 na jimilar cinikin motoci a kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
Gwamnatin Kano ta raba kayayyakin aiki na zamani na kimanin Naira Miliyan 250 ga cibiyoyin horas da sana’o’in hannu biyu da ke Kofar Mata da Gwale, domin yaƙi da shan miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a tsakanin matasa, ta hanyar samar da aikin yi.
Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Kofarmata, ya ce an amince da tallafin ne bisa umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf don bunƙasa tsare-tsaren ƙarfafa matasa a jihar.
Ya bayyana cewa an samar da injinan sarrafa fata guda 26 domin cibiyoyin wadanda al’ummar yankunan suka kafa, amma ba su da isassun kayayyakin aiki.
Ya ce Gwamna Yusuf ne ya gina Cibiyar Horaswar ta Gwale kasancewar nan ce mazabarsa, yayin da Dakta Yakubu Adam ya taka rawa wajen gina ta Kofar-Mata.
Ya ce cibiyoyin za su samar da daruruwan ayyukan yi tare da rage matsalolin zaman kashe-wando da ta’addanci a tsakanin matasa.
A nasa jawabin, Ali Musa Kofar-Mata na ƙungiyar IKMA ya gode wa gwamnati bisa wannan gudummawar da ya kira mai sauya rayuwa.
Ya ce cibiyar ta fara ɗaukar matasa maza da mata, kuma horon zai ɗauki watanni uku kafin a shiga sabon zagaye.
Abdullahi Jalaluddeen