Karon farko an tattauna kai tsaye tsakanin ECOWAS da AES
Published: 24th, May 2025 GMT
A karon farko an fara tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da ta AES ta kawancen kasashen nan guda uku na Sahel da suka balle.
Shugaban hukumar ECOWAS, dan kasar Gambia Omar Touray, ya tattauna a birnin Bamako da ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar AES wato Mali, Burkina da kuma Nijar.
Wannan dai shi ne karon farko tun bayan ficewar kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar daga kungiyar ECOWAS a watan Janairun 2024.
Bangarorin sun tattauna kan manyan batutuwan da suka hada da siyasa, diflomasiyya, shari’a, tsaro, da kuma ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
An dai amince, bisa bukatar shugabannin yankin, na kiyaye nasarorin da aka cimma a hadin gwiwar yankin, da tabbatar da zirga-zirgar jama’a da kayayyaki cikin ‘yanci, har zuwa lokacin da aka kulla sabbin yarjejeniyoyin tsakanin ECOWAS da AES.
An kuma yi tsokaci game da bukatar gaggauta yaki da ta’addanci a yayin wannan taro.
Bangarorin biyu sun bayyana damuwarsu kan wannan batu tare da cimma matsaya kan “gaggauta yin aiki don samar da yanayin da ya dace don samar da hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.”
Shugaban Hukumar ta ECOWAS da Ministocin Harkokin Waje na Kungiyar ta AES sun amince da ci gaba da yin shawarwarin “kullum bisa bukatu na jama’ar yammacin Afirka.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin HKI A Kasar Yemen
A yau Litinin ne kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa wacce ta kunshi yin Allawadai da harin ta’addancin da HKI ta kai wa kasar Yemen, wanda ya shafi tasoshin jiragen ruwa da muhimmacin cibiyoyin kasar.
Bayanin na Hizbullah ya kuma ce; Makiya suna tsammanin cewa ta hanyar wannan irin harin na wuce gona da iri za su yi hana Yemen ci gaba da matakin da take dauka na daukaka wajen taimakawa Gaza, ta daina kai hare-hare masu tsanani da take kai musu.
Haka nan kuma Hizbullah ta ci gaba da cewa: Har yanzu ‘yan sahayoniya sun kasa fahimtar dabi’ar mutanen Yamen masu hakuri da juriya akan tafarkin jihadi, domin akida ce, cewa gaskiya ita ce wacce ta cancanci a yi biyayya a gare ta, haka nan kuma kare wadanda aka zalunta.”
Kungiyar ta Hizbullah ta kuma kara da cewa; Matsayar da mutane Yemen jagorori da al’umma suke dauka, ya samo asali ne daga koyarwar Imam Hussain ( a.s) wanda ba yi sassauta akan gaskiya ba, wajen kalubalantar dawagitai.”
Kungiyar ta Hizbullah ta kara da cewa; Abokan gaba ba za su cimma manufarsu ba, kuma kamar yadda a baya Amurka ta ci kasa akan Yemen, ita ma Isra’ila makomarta kenan.