Eslami : duk wani mataki da Iran ta dauka ya dogara ne kan manufofi da muradun kasar
Published: 24th, May 2025 GMT
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) Mohammad Eslami ya ce duk wanimataki da Tehran ta dauka ya dogara ne kan manufofi da muradun kasar.
“Muna ci gaba bisa ga manufofinmu da bukatun kasa,” in ji Eslami
Babban jami’in nukiliya na kasar Iran ya jaddada cewa daya daga cikin muhimman nasarorin juyin juya halin Musulunci shi ne yadda kasar ke tsara tafarkinta da kuma yanke hukunci bisa muradun kasa.
Eslami ya bayyana cewa, a halin yanzu Iran tana matsayi mai kyau a fannin kimiyya da fasaha na masana’antu, daidai da kasashen da suka ci gaba da suka zuba jarin miliyoyin daloli.
Kafin hakan dama Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a ranar Talata ya bayyana cewa “ba daidai ba ne” a ce Amurka ta dage kan Iran ta dakatar da ayyukanta na inganta makamashin Uranium cikin lumana.
Jagoran ya ce “Babu wanda ke jiran izini daga wurin kowa, Jamhuriyar Musulunci tana da manufofinta, hanyoyinta, kuma tana aiwatar da manufofinta.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Bukaci Kada Amurka Ta Siyasantar Da Hadin Gwiwar Bangaren Ilimi
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, hadin gwiwa a bangaren ilimi tsakanin Sin da Amurka na moriyar juna ne, kuma Sin ta kasance mai adawa da siyasantar da hadin gwiwar bangaren ilimi.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai na yau Juma’a, lokacin da aka nemi jin ta-bakinta kan matakin gwmnatin Trump na hana jami’ar Harvard daukar dalibai daga kasashen waje.
A cewar Mao Ning, ire iren wadannan matakai da Amurka ke dauka za su lalata kima da darajar kasar, tana cewa, Sin za ta nace wajen kare hakkoki da muradun dalibai da malaman kasar dake kasashen waje.
Ta kuma jaddada adawar Sin ga bata sunanta da takalarta ba gaira ba dalili, tana mai kira ga Amurka ta dage takunkumanta da suka sabawa doka. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp