HausaTv:
2025-09-18@00:00:54 GMT

SojojinHKI Sun Kashe Akalla Mutane 75 A Gaza A Ranar Jumma’a Kadai

Published: 24th, May 2025 GMT

Sojojin HKI sun sabonta hare-hare a ranar Jumma’a kan fararen hula a kan Falasdinawa a Gaza, inda suka kashe akalla mutane 76 ajiya jumma’a kadai sannan wasu dadama suka ji rauni.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa sojojin HKI sun kai hare-hare a kan wani gida a Khan Yunus inda suka kashe akalla mutane.

A wani  harin da sojojin yahudawan suka kai khan yunus har’ila yau ya kashe falasdinawa akalla 8.

Alaa Al-Najjar, likita a asbitin Nasir ya bayyana cewa ta rasa yayanta har 9 a cikin asbitin sanadiyyar hare-haren HKI a kan shi.

Harin da yahudawan suka kai kan gidan Annajjar dai ya rusa gidan daga sama har kasa sannan wutan da ya taso daga gidan sai da ya watsu zuwa gidajen da suke makobtaka da gidan nata.

Dr Annajjar ta sami labarin hari a kan gidanta ne a lokacinda take aiki a kan wasu kananan yara. Yayanta sun kama daga shekara 2-16. Sannan mijinta na daga cikin wadanda suka ji rauni.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote

Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa.

Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da ƙalubale tun daga farko.

“A gaskiya tafiyar shekara ɗaya da ta wuce ta yi mana matuƙar wuya. Mun zo mu sauya tsarin kasuwancin man ƙasa. Amma wasu na ganin mun raba su da hanayar cin abinci bakinsu,” in ji shi.

’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba

Ya ci gaba da cewa, “Amma abin da muka yi shi ne mun sa Najeriya da nahiyar Afirka gaba ɗaya su yi alfahari.”

Ɗangote ya ce matatar ta riga ta fitar da lita biliyan 1.8 na man fetur zuwa ƙasashen waje cikin watanni uku da suka gabata, sannan tana da isasshen ƙarfi wajen cika buƙatar cikin gida.

Ya ce tun daga fara aikin matatar a watan Satumbar 2024, dogayen layukan man fetur da suka fi shekaru 50 ana fama da su a Najeriya sun zama tarihi.

Ɗangote ya ƙara da cewa farashin fetur ya sauka daga kusan Naira 1,100 zuwa N841 a wasu jihohi, kuma da zarar sabbin motocin gas (CNG) masu dakon mai sun fara aiki a duk faɗin ƙasar, rage farashin zai fi tasiri.

Ya kuma bayyana cewa sabbin motocin CNG 4,000 za su samar da aƙalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran ma’aikata.

“Ba mu kore kowa daga aiki ba, sai dai muna ƙara samar da ayyuka,” in ji shi.

Ɗangote ya zargi masu harkar mai da haɗa kai da ’yan kasuwa na cikin gida da na waje da ƙoƙarin hana nasarar matatar.

“Yadda aka hallaka masana’antar yadi, haka suke ƙoƙarin kashe matatar mu,” in ji shi.

A kan zargin cewa bai wadatar da ƙasa da fetur ba, sai ya mayar da martani da cewa: “Idan ba mu da ƙarfin samar da mai, me ya sa muke fitarwa zuwa ƙasashen waje?”

Ya kuma yi ba’a ga Ƙungiyar Ma’aikatan Mai (NUPENG) wadda ta ce rage farashin fetur na matatar Dangote “kyautar Girka ce.” Dangote ya ce: “Ko da kuwa kyautar Girka ce, ai kyauta ce, za ta kuma ci gaba da kasancewa.”

Ya jaddada cewa abin da Najeriya ke buƙata yanzu shi ne kare masana’antunta, domin ci-gaban tattalin arziki da kuma rage dogaro da shigo da kaya daga waje.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza.
  • Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000