Saudiya Ta Bukaci A Kafa Kasar Falasdinu Don Kawo Karshen Rigima A Gabas Ta Tsakiya
Published: 24th, May 2025 GMT
Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so.
Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu.
Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan kissan da takewa Falasdinawa a Gaza, wadanda suka ki barin kasarsu zuwa ko ina a duniya.
Manal Radwan daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiya wacce kuma take daga cikin wadanda suke shirin taron na NewYork ta fadawa majalisar kan cewa matsalolin rikicin falasdinawa da HKI suna da dama amma mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne rashin amincewa da samuwar juna.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
An garzaya da shi zuwa babban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kebbi, inda daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.
An yi jana’izarsa a babban masallacin Sarkin Gwandu, sannan aka binne shi a makabartar Dukku da ke kan hanyar Makera zuwa Kangiwa.
Jana’izar ta samu halartar jami’an kwas5tan, ‘yan uwa, abokai da sauran mu5sulmi daga sassa daban-daban na jihar.
Har yanzu al’ummar garin Filgila da kewaye na cikin tashin hankali da fargaba, kasancewar hare-haren Lakurawa na jefa su cikin zulumi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp