Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Zuba Dala Biliyan 74 A Fannin Kiwon Dabbobi
Published: 24th, May 2025 GMT
Ministan ya kuma zayyano jerin shirye-shiryen da gwamnatin tarayya ta kirkiro da nufin zaburar da matasa rungumar kiwon dabbobi, musamman don samun riba ciki har da sama musu hektar noma 51,000, a karkashin hadaka da shirin fitar da kaya na ‘Gulf’ na jihohi da kuma shirye-shiryen farfado da guraren kiwon dabbobi 417 a daukacin fadin kasar nan.
“Muna da abubuwan da za mu yi amfani da su a kasar nan, domin yakar yunwa a fadin kasar baki-daya,” in ji Ministan.
“Akalla a kasar nan, muna da Shanu kimanin miliyan sha biyar da Tumakai miliyan 60 da Kaji da miliyan 600 da Akuyoyi da miliyan 1.4 da Rakuma miliyan 700,000 tare kuma da kasar noma, amma sai dai har yanzu, kasar na shigowa da Madarar Shanu,” in ji shi.
“Wannan wata dama ce, domin abin da muke bukata shi ne, sanya wa matasan kasar karsashin rungumar kiwon dabbobi, domin samun riba,“ in ji Ministan.
Mukhtar ya kuma kalubalanci matasan kasar nan da su yi amfani da fasahar zamani wajen kiwon dabbobin, musamman domin cike gibin noman gargajiyar da ake da shi.
“Ya zame mana wajibi a yanzu a wannan fanni na kimiyya da fasaha, mu kawar da amfani da kayan aikin noma na gargajiya, kamar irin su Fartanya da sauran makamantansu.”
Ministan ya kuma buga misali da shirin ciyar da ‘yan makaranta abinci, wanda ya yi nuni da cewa; idan har za a iya amfani da shirin wajen ciyar da ‘yan makarantar firamare miliyan 47, za a iya shayar da su da Madarar Shanu rabin Lita a kullum, za a iya samun bukatar litar ta Madarar a kasar, za ta karu zuwa sama da miliyan 23, a kullum, wanda hakan zai kuma kara taimakawa wajen samar da ayyukan yi a fannin na samar da Madarar, domin samun riba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Amurka Ya Bukaci Amurka Ta Jefa Makaman Nukliya Kan Gaza
Wani dan majalisar dokokin kasar Amurka daga jam’iyyar Republican daga jihar Florida Randi Fine ya bukaci gwamnatin Amurka ta yi amfani da dimbin makaman N uklkiya da ta tara don kawo karshen yaki a gaza, ta kashe dukkan Falasdinawa a lokaci guda a huta.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Fine yana fadar haka a wata hira da ta hadashi da tashar talabijin ta Foxnews a jiya Alhamis.
Ya kuma kara da cewa Amurka bata shiga tattaunawa da sojojin Nazi a yakin dunbiya na biyu ba, bata kuma yi kome bas ai da ta yi amfani da makaman nuklioya a kan Hiroshima da kuma Nagasafi sai kasar Japan ta mika kai ba tare da wasu matsala ba.
Fine yace a yanzun ma al-amarin ya kai ga zabin amfani da Nukliya kan Gaza kawai ta rage.
Labarin ya kara da cewa wannan bas hi ne karon farko wanda Randy Fine yake kiran gwamnatin Amurka ta yi haka ba. Kuma ya sha suka daga kungiyoyi daban daban.