Leadership News Hausa:
2025-07-09@10:58:20 GMT

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

Published: 24th, May 2025 GMT

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

Mene ne burinki na gaba game da fim?

Burina shi ne a ce yau ga ni ni ma na fito da kudina a ce yau ni ce furodusa ta kaina da kaina, ina rokon ubangiji Allah ya nuna mun ranar nan inada wannan burin sosai ace ni zan yi furodusin fim dina da kaina kuma in sha Allahu muna nan muna rokon Allah yayi mana zabin abin da ya fi zama alkhairi, in sha Allah.

Wadanne jarumai ne suke burge ki tun kafin ki fara fim har ma da yanzu da ki ke cikin masana’antar su waye suka zama allon kwaikwayonki?

Zan iya ce miki ‘acting’ din kowa yana burge ni kowa da yanayin aktin din da za ka ga kawai ka yi wani abu ne karamun abu ne wanda ma bai burge wancen ba amma ni ya burge ni, kowa yana burge ni, kuma kowa jarumi na ne kowa na burge ni cikin ikon Allah.

Wane ne ubangidanki a cikin masana’antar kannywood?

Ubangidana babana maganin kuka na, ai ni ubangida na rage masa baba ne, kamar mahaifi na dauke shi, Baba Falalu, Falalu A. Dorayi shi ne komai na a ‘industry’.

Da yawa wasu daga cikin ‘yan kannywood za ki ji suna cewa akwai karancin girmamawa ga na kasa zuwa ga na sama, me za ki ce a kan hakan?

Allah ya shirye mu gabadaya, amma ni dai gaskiya duk wanda ya sanni ya san ina girmama na sama da ni kuma har na kasa da ni, saboda zan iya ce miki ni ko mutum ya girme ni ko da kani gare ni ni ban ma iya kiran sunan shi sai dai in dauki wani abun in laka masa, ko in ce dan’uwa ko na ce yayana na san ka girme ni amma sunan naka ne ba zan iya kira ba, gaskiya ni bana daga cikin wadannan wanda ba sa darajanta na sama gare su, kuma ina fatan ubangiji Allah ya shirye mu gabadaya, saboda in ka darajanta wani kanka ka darajanta shi ne kawai.

Idan aka ce ki fadi abu daya wanda sam bai yi miki ba a cikin masana’antar kannywood wane abu za ki ce?

Abu daya da zan ce shi ne zan iya cewa dan Allah mu kaunaci junanmu gabadaya, mu so junanmu gabadaya

Ya batun aure shin kin taba yin aure ko kuwa tukunna dai, kuma yaushe ki ke saka ran yin aure?

A’a ‘yar’uwa ban taba yin aure ba amma addu’ar mu kenan muna rokon Allah ubangiji ya kawo mana miji nagari wanda in muka shiga mun shiga kenan [Dariya]… mutu-ka-raba, kuma sai a taya mu da addu’a.

Shin za ki iya auren abokin aikinki dan fim, ko kuwa ba ki da irin wannan ra’ayin?

Eh! sosai, wallahi sosai zan iya indai yana sona ina son shi lafiya lau zan aure shi, kuma mu zauna cikin ikon Allah, wallahi zan iya.

Misali a ce kin yi aure kin haifi ‘ya, kuma tana son yin fim shin za ki bar ta ta yi ko kuma ba ki da ra’ayin hakan?

‘Yar’uwa indai nayi aure na haifi ‘ya tana so zan bar ta, ni fa fim sana’a na dauke ta, wallahi sana’a babba na dauke ta, wanda ake ci gaba a cikinsa, ban dauki fim da wasa ba da gaske na dauke shi, saboda na san har da zuciyata ni sana’a na dauke ta kuma sana’a nake to, wallahi wallahi har da zuciyata nake fito miki da maganar wallahi tallahi indai ‘ya ta za ta yi cikin ikon Allah ni zan rika ma kai ta lokeshan din, zan je na kai ta na jira ta ko in je idan ta gama na je na dauko kaya ta karshe kenan.

Wacce shawara za ki bawa masu kokarin shiga fim har ma da wadanda ke ciki abokan aikinki?

Shawarar da zan bawa wanda suke tasowa da mu gabadaya har da ni me magana shi ne; ka san kanka, ka san darajar kanka, ka san na iyayenka, ka san na wanda ka ke rayuwa da su, kar ka yi abin da mutuncinka ya zube ko na ‘yan’uwanka ko na iyayenka ko ma dai kawayenka ace yau kana tare da wani a dalilinka ace ai wane ka-za ka-za yayi, a’a sai mun duba mun ga abin da ya dace duk abin da bai dace ba kar ma ka yi fostin din shi da za ka jawo wa kanka magana ko surutu ce-ce kuce, dole wani abu sai muna yi muna dubawa. Muna fatan kafin mu yi shi Allah ya kare mu duk wani abu da zai janyo mana zagin iyayen mu, ‘yan’uwan mu, Allah komai dadin shi ubangiji Allah kar ka ba mu ikon yin shi alfarmar Annabi Muhammad (s.a.w).

Me za ki ce ga jaridar Leadership Hausa har ma da wannan shafi na Rumbun Nishadi da sauran al’ummar da suke karanta wannan hirar taki?

Ina yi musu fatan alkhairi ubangiji Allah ya kara dauka su, Allah ya kara darajntasu a idon duniya gabadaya, Allah ya sa musu hannu a inda suke iyawa da inda ba sa iyawa, kuma ubangiji Allah ya yi musu abin da mai zato bai taba tsammani ba na alkhairi, tsakanina da su sai dai nayi fatan alkhairi, ina fatan alkairi a gare su sosai-sosai.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ba zai wuce masoya, ‘yan’uwa, da kowa da kowa ba, ina yi wa kowa da kowa fatan alkhairi ubangiji Allah ya bar mu tare, ya bar zumunci kuma roko na guda daya ga masoyana ‘yan’uwana duk wani abu ni dai Hauwa Ayawa kofa a bude take, socual media na za ka iya yi mun DM cikin ikon Allah zan yi maka ‘reply’ duk wani abu da ku ka ga nayi wanda bai dace bai kamata ba dan Allah dan Annabi ku bani shawara zan gyara cikin ikon Allah, dan Allah dan Annabi duk me nayi wanda ku ke ganin zai zubar da mutunci, ah wannan abu bai dace Hauwa’u tayi ba dan Allah dan Annabi ku bani shawara kuma zan yi zan bi, in sha Allahu, na gode Allah ya bar mu tare. Allah ya daukaka mu gabadaya kuma Allah ya kawo mana mazajenmu nagari.

Muna godiya, ki huta lafiya

Ni ma na gode sosai.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: ubangiji Allah ya mu gabadaya

এছাড়াও পড়ুন:

Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC

Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025.

 

Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano.

 

Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara.

 

Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa.

 

 

“cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da suka shafi take hakkin dan adam”

 

 

A cewar Alhaji Shehu, yanayin zamantakewar al’umma a halin yanzu yana nuni da yadda ake tauye hakkin yara, wanda hakan ya nuna yadda ake kara yawaitar yaran da ke yin bara a tituna da kuma rayuwa cikin mawuyacin hali.

 

“Sakaci na iyali da al’umma shi ne babban abin da ke haifar da cin zarafin yara da kuma karuwar ayyukan aikata laifuka a tsakanin matasa.”

 

Ko’odinetan hukumar ta NHRC ya jaddada cewa, yayin da bakwai kawai daga cikin wadanda aka bayar da rahoton an aikata su ne ta hannun masu  fada aji kuma yana farywa a cikin gidajen aure.

 

“Iyali su ne tushen al’umma, al’umma kuma ita ce al’umma, saboda haka, duk wani cin zarafi a cikin iyali zai yi naso a kan al’umma baki daya.”

 

Ya kara da cewa “Lokacin da aka samu babban cin zarafi a cikin iyali, ba za a iya samun ci gaba mai ma’ana a cikin al’umma mafi girma ba.”

 

Alhaji Shehu ya ci gaba da cewa, daga cikin korafe-korafen da aka samu, an gudanar da cikakken bincike da kuma kammala shari’o’i 341, yayin da 105 ke ci gaba da sauraron karar.

 

Ya yi kira ga jama’a da su samar da zaman lafiya da juna tare da kai rahoton duk wani da ake zargi da take hakkin dan Adam ga hukumomin da abin ya shafa.

 

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, NHRC tana aiki ne a matsayin wata hanya mai zaman kanta don tabbatar da mutuntawa, kariya, da kuma inganta hakin bil’adama a Najeriya.

 

Khadija Aliyu

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • DAGA LARABA: Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu?
  •  Wani Fim Din Iran Mai Ya Sami Kyauta A Baje-Kolin Fina-finai Na Shanghai
  • Ahmed Musa Ya Ƙaryata Kyautar Motoci Ga Ƴan Wasa Da Ma’aikatan Kano Pillars
  • Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi
  • Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
  • Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC
  • Turji: Sai ka sako mutanen da ka sace za a yi sulhu — Gwamnatin Sakkwato
  • Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
  • Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano
  • Mutun 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano