Rasha Ta Tarwatsa Makaman Ukiraniya A Tashar Jiragen Ruwa Ta Odessa
Published: 25th, May 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100 dake dauke da makamai a tashar jiragen ruwa ta Odessa.
Sanarwar ta kuma kunshi cewa makaman da sojojin na Rasha su ka tarwatsa sun hada kananan jiragen ruwa na yaki na kai farmaki da ba su da matuki, jiragen sama marasa matuki, da kuma albarusai.
Sanadiyyar wannan harin harshen wuta ya tashi wanda ya dauki lokaci yana ci.
A gefe daya an yi musayar fursunoni a tsakanin sojojin Rasha da kuma na Ukiraniya wanda shi ne mafi girma tun da yaki ya barke a tsakanin kasashen biyu.
A wani gefen, har yanzu ana ci gaba da Magana akan tsagaita wutar yaki, da Amurka take son ganin ya faru, saboda kare manufofinta na dibar albarkun kasar ta Ukiraniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Harin HKI A Kasar Yemen
A yau Litinin ne kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa wacce ta kunshi yin Allawadai da harin ta’addancin da HKI ta kai wa kasar Yemen, wanda ya shafi tasoshin jiragen ruwa da muhimmacin cibiyoyin kasar.
Bayanin na Hizbullah ya kuma ce; Makiya suna tsammanin cewa ta hanyar wannan irin harin na wuce gona da iri za su yi hana Yemen ci gaba da matakin da take dauka na daukaka wajen taimakawa Gaza, ta daina kai hare-hare masu tsanani da take kai musu.
Haka nan kuma Hizbullah ta ci gaba da cewa: Har yanzu ‘yan sahayoniya sun kasa fahimtar dabi’ar mutanen Yamen masu hakuri da juriya akan tafarkin jihadi, domin akida ce, cewa gaskiya ita ce wacce ta cancanci a yi biyayya a gare ta, haka nan kuma kare wadanda aka zalunta.”
Kungiyar ta Hizbullah ta kuma kara da cewa; Matsayar da mutane Yemen jagorori da al’umma suke dauka, ya samo asali ne daga koyarwar Imam Hussain ( a.s) wanda ba yi sassauta akan gaskiya ba, wajen kalubalantar dawagitai.”
Kungiyar ta Hizbullah ta kara da cewa; Abokan gaba ba za su cimma manufarsu ba, kuma kamar yadda a baya Amurka ta ci kasa akan Yemen, ita ma Isra’ila makomarta kenan.