Aminiya:
2025-07-09@06:57:40 GMT

An fara aikin gina mayankar dabbobi ta Naira biliyan 3 a Gombe

Published: 24th, May 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe.

Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar.

An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025.

An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar.

Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 5 a Borno Yadda dilolin ƙwaya ke cin karensu ba babbaka a Abuja

“Wannan ba kawai wurin yanka dabbobi ba ne, amma zuba jari ne ga ci-gaban kiwon dabbobinmu. Za mu tabbatar da aiki da ka’idojin duniya wajen tsafta, yanka, da sarrafa nama,” in ji shi.

Farfesa Abubakar ya kuma yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya saboda hangen nesansa wajen kyautata kayan more rayuwa da bunkasa tattalin arzikin jihar.

Shugaban gudanarwa na kamfanin Lubel Nigeria Limited, Akitet Yunusa Yakubu, ya yi alkawarin kammala aikin cikin inganci da kuma a kan lokaci, tare da alkawarin cika dukkan sharudda domin tabbatar da nasarar aikin.

Da zarar an kammala wannan mayankar dabbobi na zamani, ana sa ran zai kawo sauyi mai amfani ga harkar sarrafa nama a Jihar Gombe, da rage hadarin rashin tsafta da ke tattare da hanyoyin gargajiya, tare da samar da damammaki a cikin darajar kiwon dabbobi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: mayanka

এছাড়াও পড়ুন:

An ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutum 38,000 a Yobe

Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe.

Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan kasa da shekaru biyar sama da 38,000 a fadin jihar.

Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya

Gwamnan ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba yayin da ya kaddamar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin fadada harkokin kiwon lafiya, musamman ga marasa galihu.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin jawabinsa a wajen babban taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Damaturu, wanda ya samu halartar sarakunan gargajiya da malaman addini, abokan hulda, ma’aikatan lafiya da manyan jami’an hukumar gudanarwa a bangaren samar da kiwon lafiya a matakin farko da kuma kungiyoyin farar hula.

Gwamna Buni ya bayyana manufarsa ta samar da lafiya mai rahusa a matsayin ginshikin ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma.

Ya amince da goyon bayan gwamnatin tarayya da abokan hulda da suka hada da Gidauniyar Bill and Melinda Gates, Aliko Dangote Foundation, UNICEF, da WHO da dai sauransu.

Gwamnan ya jaddada kudirin jihar na samar da kiwon lafiya, inda ya ba da misali da kafa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 142, samar da kayan aiki da magunguna, da daukar kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sama da 2,000 a fadin Jihar.

Ya bayyana irin nasarorin da jihar ta samu ciki har da fitowar ta a matsayin zakara ta shekarar 2024 a bangaren samar da kiwon lafiya a matakin farko a fadin kasar nan ta Champion leadership for Primary Health Care PHC  2024.

Ya kuma yi tsokaci kan kafa Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Jihar Yobe (YSCHMA) da Hukumar Kula da Magunguna ta Jihar Yobe (YODMA) don magance kuɗaɗen kula da lafiya da samar da magunguna.

Kazalika, ya bukaci sarakunan gargajiya da su ba da goyon baya tare da bayar da gudunmawa wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a yankunansu.

Gwamnan ya bukaci masu ruwa da tsaki da su lura da batutuwan da aka tattauna a taron tare da magance kura-kuran da ake da su a yankunansu da kuma wuraren gudanar da ayyukansu domin kara inganta harkar kiwon lafiya a matakin farko a Jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Ware Yuan Biliyan 10 Don Shirye-Shiryen Ba Da Tallafin Aiki
  • ‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’
  • ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Nijeriya
  • An ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutum 38,000 a Yobe
  • Sin Za Ta Gina Wuraren Cajin Ababen Hawa Masu Ingantaccen Lantarki
  • An ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutum 38,000 a Gombe
  • Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Aikin Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%
  • Asibiti Mai Zaman Kansa A Kano Zai Fara Manya Manyan Tiyatu Tare Da Rage Kuɗi Kaso 50%
  • Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa ta Kwace Gurbatattun Kayayyaki na Miliyoyin Naira
  • Mataimakin Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Sabbin Fasahohin Kimiyya A Fannin Aikin Gona Da Kiwon Lafiya