Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a Ilori
Published: 24th, May 2025 GMT
Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB) ta sanar cewa mutanen da suka tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Kwara suna samun kulawa a asibiti
Da yake tabbatar da cewe duka mutanen cikin jirgin horon sun tsira da ransu, Babban Daraktan NSIB, Kyaftin Alex Badeh Junior, ya ce hukumar ta gano katin nadar bayanai daga jirgin, bayan aukuwar hatsarin a filin jirgin sama na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilorin,
Jirgin, nau’in Diamond, mai lamba BNI, mallakin Kwalejin Koyon Tukin Jiragen Sama ta Ilorin (IAC) ne, kuma ya yi hatsarin ne a yayin atisayen sauka na gwaji, inda ya kauce daga titi, ya yi cikin daji ya lalace fiye da yadda za a iya gyarawa.
Kyaftin Badeh ya bayyana Ya ce wadanda ya yi hatsari da su sun hada da shugaban horo, wanda aka sani da Ajape, da wata daliba, Lola. Dayansu ya samu rauni mai tsanani, ɗayan kuma ya samu raunuka marasa yawa, kuma dukansu suna karbar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH).
Hakar man Kolmani: Jihohin Bauchi da Gombe sun gana da NNPC kan bukatun al’umma Za mu gina mayankar dabbobi a kan Naira biliyan 3 a Gombe —GwamnatiYa bayyana cewa ana nazarin katin bayanan da aka gano a dakin gwaje-gwajen NSIB, kuma ana sa ran za a fitar da rahoton farko cikin kwanaki 30 masu zuwa.
Ya jaddada cewa aikin hukumar shi ne gano abin da ya faru da kuma yadda za a hana sake faruwar irinsa a nan gaba, yana mai tabbatar wa jama’a cewa duk da hatsarin da ya faru, sararin samaniyar Najeriya yana nan cikin aminci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hatsarin jirgi
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar.
A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai 6 sannan wasu 22 suka ji rauni.
Yankin Sistan Baluchistan dai ya dade yana fama da hare-hare na wannan kungiyar, kuma tana da sansani a cikin kasar Pakistan wacce take makobtaka da kasar a kudu maso gabacin kasar.