Yara Miliyan 2.9 A Nijeriya Ke Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki – UNICEF
Published: 24th, May 2025 GMT
UNICEF ta gabatar da asusun abinci na yara don karfafa zuba jari a cikin manufofi da shirye-shirye. UNICEF ta jajirce wajen yin hadin gwiwa da gwamnatin Jihar Kwara don yaki da rashin abinci mai gina jiki, musamman a lokacin kwana 1000 na farko na rayuwar yara.
“Kalubalen shi ne, yawan yara fiye da kashi 40 cikin 100 suna da gwannan matsala kuma kusan yara 300,000 suna fuskantar samun kulawar gaggawa don magance wadannan matsaloli.
Ta danganta dalilan rashin abinci mai gina jiki ga sakamakon talauci, canjin yanayi, rashin samun abinci, da kuma matsalolin tsaro.
A nasa jawabin, Gwamna Jihar Kwara, AbdulRaman AbdulRazak, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Jubril Shaaba Mamman, ya bayyana cewa, tasiri mai kyau game da rayuwar yara na Jihar Kwara shi ne, samun abinci mai gina jiki, wanda wannan ya sa aka yanke shawarar karbar shirin asusun samar da abinci mai gina jiki ga yara na UNICEF.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yara
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu.
An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda wani ɗan uwansu ya bayyana wa Aminiya.
Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?“Alhamdulillah! Anas, Halimatu da ’yarsu sun kuɓuta. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida, amma sai da aka biya ’yan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi.
An sace su ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2025 a gidansu da ke Filin Canada Quarters, a Jihar Katsina.
Da farko, mahafan sun nemi Naira miliyan 600, daga baya suka rage kuɗin zuwa miliyan 100, sannan daga ƙarshe suka amince aka biya su miliyan 50.
Saboda dalilan tsaro, ’yan uwansu ba su bayyana inda aka sako su ba.