Hamas: Za A Yi Musayar Fursunoni Kamar Yadda Aka Tsara
Published: 13th, February 2025 GMT
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa.
A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara.
Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na kiwon lafiya na gaggawa.
Wasu daga cikin matsalolin da aka warware sun hada bayar da damar shigar da manyan kayan aiki da motocin buldoza na kwace baraguzai, da makamashi, da kuma magunguna.
Sanarwar da kungiyar ta Hamas ta wallafa a shafinta na “Telegram” ta ambato masu shiga tsakani da su ne kasashen Masar da Katar suna cewa, za su sa ido domin ganin cewa ana aiki da abubuwan da aka yi yarjejeniyar akansu.
Wannan matakin na kungiyar Hamas, ya zo ne bayan da a kwanaki kadan da su ka gabata ta sanar da dakatar da batun sakin fursunonin har illa masha Allah, saboda yadda HKI take take sharuddan yarjeniyar da aka cimmawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai
A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana.
An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida.
DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a BornoPSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba.
Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0 a Emirates a cikin watan Oktoba.
Arsenal da Paris Saint-Germain da Inter Milan da Barcelona su ne kungiyoyin da 4 da suka kai matakin zagayen daf da karshe na gasar.
A wannan Larabar ce kuma za a yi karon batta tsakanin Inter Milan da Barcelona, bayan kimanin shekara 15 da aka yi makamancin wannan karawar daf da karshe tsakanin ƙungiyoyin biyu a Gasar Zakarun Turai.
Inter Milan ce ta kai zagayen ƙarshe a 2010, sai dai wannan karon Barcelona na fatan lashe kofin bana da zarar ta fuskanci Arsenal ko Paris St Germain a watan gobe.
Sai dai, Barca da Inter sun fuskanci juna a gasar ta zakarun Turai a 2022/23, inda ta Italiya ta yi nasara 1-0 cikin Oktoban 2022 a wasa na biyu suka tashi 3-3 a Sifaniya.
Wannan shi ne karon farko da Barcelona ke fatan kai wa karawar ƙarshe a Champions League, tun bayan da ta lashe na biyar jimilla a 2015.