Aminiya:
2025-05-24@11:56:42 GMT

Mace ta damfari masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 250

Published: 24th, May 2025 GMT

Wata mata da ta yi wa masu neman aikin gwamnati damfarar kudi sama da Naira miliyan 250 ta shiga hannun jami’an tsaro.

’Yan sanda sun cika hannu da wannan mata mai suna Iyabode Oluwafemi ne a Jihar Ondo bisa zargin karbar kudaden ta hanyar yaudarar mutane da ta yi wa alkawarin sama masu ayyuka a ma’aikatu da hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban.

A yayin da da yake magana kan wadda ake zargin a ofishinsa da ke Akure, babban birnin jihar, Kwamishinan ’yan sanda a jihar, Wilfred Afolabi, ya ce jami’an runduanr sun yi nasarar kama Iyabode Oluwafemi ne bayan yawan korafin da mutanen da ta damfara suka yi.

Ya bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da ita gaban kotu domin yanke mata hukunci.

An kama yarinya kan kashe jariri a sansanin ’yan gudun hijira An kama jami’in Hukumar NRC da laifin satar waya

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wadda ake zargin, amma kakakin ’yan sanda na Jihar Ondo bai amince da zantawa da ita ba saboda a cewarsa yin hakan zai iya janyo koma-bayan binciken da suke yi.

Yadda ake damfarar masu neman aikin gwamnati

Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna ana samun karuwar matasa maza da mata da suka kammala karatu, da ke neman aikin gwamnati ta bayan fage, ko haramtattun hanyoyi.

Daga cikinsu akwai ’ya’yan masu madafun iko da iyayensu suke amfani da matsayinsu wajen tilasta ba su ayyukan gwamnati ga. Akwai kuma ’ya’yan masu masu kumbar susa da suke biyan kudaden da suka kama daga naira miliyan daya zuwa sama a matsayin na-goro domin sayen guraben aiki.

Marasa galihu kuma sukan yi kundumbala, inda wasu ke ciwo bashin kudi da gwanjatar da ’yan abin da su ko iyayensu suka mallaka domin cimma wannan buri, da alkawarin biya idan sun samu.

Wasu mata daga cikinsu sukan ba da kansu, ko su yi yawon karuwanci domin kawai su samun abin da za su yi domin samun aikin gwamnati.

A gefe guda kuma, akwai jami’an gwamnati da dillalai masu karbar makudan kudade daga hannun irin wadannan matasa, bisa alkawarin sama masu aikin.

Wani lokaci dillalan kan yi nasarar sama wa matasan aiki bayan kulla cuwa-cuwa a tsakaninsu da wasu jami’ai da ke kula da daukar sababbin ma’aikata a matakin gwamnati a matakin jihohi ko tarayya. Amma a wasu lokuta kuma sukan yi batar kakatantan.

Dillalan aikin gwamnati ‘sun wanke’ ni

Wata matashiya mai shekaru 35 da ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana wa Aminiya yadda ta tashi ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko bayan ta fada a hannun masu damfarar masu neman aiki bayan ta kammala karatu.

Ta bayyana cewa, “Na yi gwanjon wasu kadarorin da na yi gado daga mahaifina wajen biyan kudin karatun jami’an, inda na samu digiri a fannin Ilmin Lafiyar Dabbobi, amma na ci karo da matsalar samun aiki.”

Ta ce daga baya, “Na samu labarin wadannan dillalan bogi da mahaifiyata ta amince da mu sake gwanjatar da kadarorinmu domin biyan su kudi Naira miliyan daya da dubu dari baiyar da suka nema daga gare ni da alkawarin sama min aikin gwamnati.”

A karshen bayanin da hawaye ke zuba a fuskarta cewa ta yi, “Bayan na kammala biyan kudin baki daya sai na daina ganin su a wurin da muka saba haduwa, wanda a karshe na shiga matsananciyar damuwa da ba zan taba mantawa da ita ba domin sun yi layar zana ban san inda zan gano su ba.”

‘Akwai hadin bakin jami’an gwamnati’

Wani tsohon ma’aikacin gwamnati da aka sakaya sunansa, ya ce “Son zuciya da dogon buri daga bangaren manyan ma’aikatan gwamnati ne yake haifar da irin wannan cuwacuwar cefanar da guraben aiki ga daliban da suka kammala karatu.

“Za ka ga cewa da zarar an samu gurbin daukar sababbin ma’aikata sai Babban Sakatare a wannan ma’aikata ya tura ’yan korensa daga cikin kananan jami’an da suke aiki a karkashinsa su fara tuntubar dillalan bogi suna bibiyar dalibai da suke karbar dimbin kudade a hannunsu da suke yin kashe-mu-raba a tsakanin su.”

Ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun sha gargadin masu neman aiki da su guji bi ta bayan fage ko abin da zai jefa su a hannun ’yan damfara, musamman a lokacin da cibiyoyin gwamnatin suka sanar da shirin daukar ma’aikata ko aka fara jitajitar hakan.

Hukumomin yaki da ayyukan danfara da dangoginsu sun sha kamawa tare da hukunta irin masu wannan aiki, wani lokaci, hukumomin da abin ya shafa sukan kama tare da hukunta jami’an da abin ya shafa, amma har yanzu ana samun masu kunnen kashi, kuma masu neman aiki ba su daina fadawa a tarkonsu ba.

A kan yadda a wasu lokuta ake kama irin wadannan mutane ba tare da hukunta su ba, sai tsohon ma’aikacin ya ce “tun farko na gaya maka cewa daga sama suke samun daurin gindi daga bangaren manyan ma’aikata.

Abin da ke jefa matasa a tarkon ’yan damfara

Wani mai fashin baki da ke zaune a birnin Akure, Kwamared Ibrahim Shu’aibu, ya ce “Wannan lamari ya zama abin kunya da tausayi da bakin ciki har da mamaki inda mahukunta Nijeriya suke kallon irin barnar da ake yi, wacce ta zama ruwan dare ba tare da daukar matakin shawo kanta ba.”

Kwamared Ibrahim Shu’aibu ya danganta yadda matasa ke fadawa a hannun irin wadannan bata-gari da gaggawa da neman cin bulus. Ya ce, “Mafi yawanci sun taso ne ba tare da koyon kananan ayyuka da sana’o’in dogaro da kai, lamarin da ya taimaka wajen kashe guiwar dalibai, musamman ’yan Arewa da suka fi mayar da hankali wajen dogaro da samun aikin gwamnatoci domin cin banza a maimakon rungumar kananan ayyuka da sana’o’i da kasuwanci da zai taimaka masu dogaro da kansu kamar yadda dalibai a sashen Kudancin kasa suke yi.

Ya ce, “Irin wannan lamari ya zama ihu bayan hari ga Arewa. Gwamnatocin baya sun samu damar hana ci gaba da aukuwar irin wannan barna a zamaninsu sai dai sun yi sako-sako da suka bari lamarin ya ci gaba har zuwa wannan zamani da ’yan siyasa suka kara dagula al’amura.

Mai fashin bakin ya ce “wani abun takaici shi ne yadda za ka ga matasan da suka kammala karatu na da jarin sama da naira dubu 200 a hannunsu amma sun kasa shiga kananan kasuwanci su juya wannan kudin, sun fi so su yi amfani da wannan kudi wajen neman aikin gwamnati da yunkurin fita zuwa kasashen Turai.”

Yadda za magance matsalar

Kwamared Ibrahim ya ce, “muhimmin abun da zai taimaka wajen samun saukin irin wannan tabargaza a tsakanin matasa masu neman aikin gwamnati da dillalan bogi masu karbar miliyoyin kudi daga hannunsu shi ne gwamnatin kasa ta tabbatar da samar da guraben aiki da yin adalci ga miliyoyin matasa domin akwai arzikin da za a iya daukar wannan nauyi.

“Su kuma masu rike da madafun iko su sanya tsoron Allah a kan abun da suke yi wanda yake kara kyamar juna a tsakanin ’yan Najeriya.

“Kuma a tabbatar da hukumta dukkan mai karba da mai bayarwa a domin dukkan su suna da laifi,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Damfara gwamnati masu neman aikin gwamnati kammala karatu gwamnati da an gwamnati irin wannan

এছাড়াও পড়ুন:

Mayar Da Hankali A Aikin Farfado Da Kwararrun Asibitocin Gwamnatin Tarayyya

Matakin da Gwamnatin ta dauka, na son yin amfani da Gidauniyar TETFund, domin yin wannan aikin, babban abin jinjinawa ne, wanda idan har ba a samu wata gazawa ba, kamar a sauran ayyukan baya, musamman duba da cewa, Giduaniyar ta samu shedar cewa, ba a santa da gazawa, wajen wanzar da ayyukan da shirye-shiyen da ta sanya a gaba, kan batun ganin an inganta karatu a jami’oin kasar.

Kazalika, Ministan ya ce, daukacin aikin shi ne, domin a dakile yawan ficewar da kwararrun Likitocin kasar ne yi ne, zuwa ketere domin neman aiki, wanda hakan zai sanya, a ciki gaba da raike su a kasar nan, domin su yi aki a cikin kasar.

A karkashin aikin, za a kuma tabbatar da an samar da kayan aiki da samar da masu da karin kudade da kuma kara inganta yanayin mai kyau, da za su gudanar da ayyukansu, na duba marasa lafiya.

Alausa ya ci gaba da cewa, daukin da za a samar a fannin na kiwon lafiyar kasar, za a samar da shi ne, ga manyan bangarorin kimiyya, samar samar da magunguna da na jinya.

A cearsa, za a wanzar da wannan zuba hannun jarin ne, a fannin na zuwa shekaru biyar wanda aka kiyasta, za a kashe kudin da ya kai Naira tiriliyan 1.5 wanda za iya cimma hakan ne, ta hanyar wanzar da shiye-shiyen.

Sai dai, tun fil azala, kalubalen da kasar ke fuskanta shi ne, na Nijeriya na yin sakaci, wajen rashin wanzar da shirye-shiyen da aka dauka

Karin wani abin takaicin shi ne, fannin kiwon lafiyar kasar, musamman a kwararrun Asibitocin, sun koma tamkar abin damauwa ga ‘yan Nijeriya da kuma su kwararrun Likitocin, duba da yadda aka yi watis da ba su kulawar da ta kamata da yawan samun aikata badakalar cin hanci da rashawa, wanda hakan ya kara durkusar da fannin na kiwon lafiyar, wanda kuma hakan ya janyo, ba sanar inganciyyar kula da kiwon lafiyar da ya dace da kuma samar da ilimantar wa.

A nan za mu iya cewa, ya kamata Gwamnati baya ga samar da kayan aiki a Asibitocin, t ya kuma zama wajbi, ta zabo wasu Makarantun horas da kwararun Likitoci domin a daga darajar Makarantun.

Kwararrun Asibitocin kasar nan dai, sun jima da lalacewa da rashin ingantattun kayan aiki duba da cewa, ba su da Gadajen kwantar da marasa lafiya da suka wuce, goma kacal.

Akasarin ‘yan Nijeriya da ke bukatar a duba lafiyarsu, suna yin tururuwa zuwa kwararrun Asibitocin kasar, amma matsalar, suna shafe awowi, domin neman Gadon da za a kwantar da su don su yi jinya.

A wasu lokacin samun Asibtin, ya danganta ne da irin karfin iko da mai bukatar yake da shi.

Domin a dakile wannan matsalar, muna kira ga Gwamnati da mahukunatn irin wadannan kwararrun Asibitocin na Gwamnati, da su tabbtar da suna tattala kudaden da ake ware masu, a cikin kasafin kudin kasa, ba wai kawai batun yiwa Asibitocin garanbawul bane, amma a samar da kayan aiki na zamani, musamman mayar da hankali kan jin dadi da walwalar kwararn Likitocin.

Hakazalika, dole ne Gwamnati ta tabbatar da wanzar da samar da ingantaccen albashi, da samar da kyakyawan yanyin aikin aiki na kwararun Likitocin kasar, wanda hakan zai ba su damar samar da sakamako mai kyau, da ake bukata a fannin.

A saboda wadannan dalilan, ya zama wajibi, Gwamnatin Tarayya da rinka yin aiki kafada da kafada da kwararrun mahukuntan kiwon lafiya da sauran amsu ruwa da tsaki domin a samar da wata manhaja kan wannan aikin tare da cimma kudurin da aka sanya a gaba, kan lokaci.

Ya kamata a zuba hannun jari wajen bai wa kwararrun Likito horo domin a inganta kwarewarsu da kuma walwalarsu.

Bugu da kari, akwai bukatar a wadatar da Asibitocin kasar da kayan aiki na zamani, musamman domin a samu damar ci gaba da duba lafiyar marasa lafiya da kuma ilimantar da kwararrun Likitocin.

Ya kuma wajaba a samar da kayaan aiki na zamani da za a rinka duba manyan larorin cuttuka, kamar irinsu, Cutar Daji, wanda hakan zai sanya, masu irin wadannan larorin, ba sai sun fita zuwa Asibicin da ke ketare, domin neman lafiya ba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Saudiya Ta Bukaci A Kafa Kasar Falasdinu Don Kawo Karshen Rigima A Gabas Ta Tsakiya
  • Faduwar Jarrabawar JAMB Ta Tayar Da Bukatar Neman Sake Fasalin Hukumar
  • Za Mu Ci Gaba Da Aikin Neman Man Fetur Arewacin Nijeriya — Ojulari
  • Ko Kwamitin Saraki Zai Iya Ceto PDP Daga Rikicin Cikin Gida?
  • Mayar Da Hankali A Aikin Farfado Da Kwararrun Asibitocin Gwamnatin Tarayyya
  • ‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Sun Kammala Aiki A Wajen Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin
  • Ma’aikatan Wutar Lantarki A Katsina Sun Tsunduma Yajin Aiki
  • Jirgin Karshe Na Alhazan Jihar Kwara Ya Isa Kasa Mai Tsarki
  • Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano