Hamas ta yi tir da kiran da dan majalisar dokokin Amurka ya yi na kai farmakin nukiliya a Gaza
Published: 24th, May 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu ta yi kakkausar suka kan kalaman baya-bayan nan da dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican Randy Fine ya yi, wanda ya yi kira da a kai wa zirin Gaza hari da makamin Nukiliya.
Kungiyar Hamas, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana kalaman dan ‘majalisar a matsayin “laifuffuka” da kuma nuna wariyar launin fata na wasu sassan Amurka.
Kungiyar ta bukaci hukumomin Amurka da na majalisar dokokin kasar da su fito fili su yi Allah-wadai da irin wadannan kalamai.
Hamas ta jaddada cewa furucin dan majalisar Republican na nuni ne karara ta keta dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kuma yana nufin tunzura kai tsaye don amfani da makaman kare dangi kan fararen hula fiye da miliyan biyu a Gaza.
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta bayar da sammacin kame a watan Nuwamban da ya gabata ga firaministan Isra’ila Netanyahu da tsohon ministan harkokin soji Yoav Gallant, bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Har ila yau Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan kiyashi a kotun kasa da kasa kan yakin da ta yi kan yankin gabar tekun da ta yi wa kawanya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar China Ta Yi Watsi da Barazanar Trump Na Kakabawa Kasashen BRICS Karin Takunkuman Tattalin Arziki
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta zargi kasar Amurka da nuna adawa da kungiyar BRICS ta raya tattalin arziki na kasashen kungiyar ta kuma kara da cewa kokarin kare kanta da ga shirye-shiryen BRICS ba zai amfane ta ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar China na cewa kungiyar kungiya ce wacce bata son babakere da Amurka take nunawa a yadda take tafiyar da al-amura a duniya kamar Ita ce, take iko da kowa.
Tace kungiyar tana son duniya ta zama mai kudubobi, wadanda su ma za’a iya fada su kuma aikata abinda suke so karkashin dokokin duniya. Don haka mamayar da takardan dalar Amurka ta yiwa mafi yawan harkokin kasuwanci a duniya bai yi masu ba. Sauran kasashen ma suna da kudade suna kuma son ganin sun fita daga danniya da babakeran da Amurka take ya a duniya.
Dole ne duniya ta zama mai kubobi, sai dai a yi aiki tare don tafiyar da al-amura a cikinta.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump bayyana cewa zai kakabawa kasashen da suke cikin kungiyar BRICS takunkuman karin kodin fito na kasha 10% don kare kasar Amurka.