Dan majalisar Amurkan mai suna Randall Adam Fine wanda yake wakiltar jam’iyyar “Republican”  ya sake tunanowa duniya  da yadda kasarsa Amurka ta jefa wa biranen Nagasaki da Hiroshima bama-baman Nukiliya a karshen yakin duniya na biyu, ta hanayr yin kira da a jefa wa zirin Gaza irin wadannan makaman na kare dangi.

Kungiyoyin Falasdinawa mabanbanta sun yi tir da wannan irin kira na ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kare dangi, suna masu yin kira ga ita kanta majalisar Amurka da ta fito da yi Allawadai da wannan  kira wanda yake cike da kiyayya.”

Kungiyar Hamas ta bayyana abinda dan majalisar na Amurka ya yi da cewa, ya keta dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kamar  kuma yadda yake a matsayin yin kira da a yi wa fiye da fararen hula miliyan daya kisan kiyashi.

Ita kuwa kungiyar jihadul-Islami ta bayyana cewa; Muna daukar kira irin wannan a matsayin yin zuga a fili da a tafka laifi akan bil’adama, sannan kuma abin kunya ne ga ita kanta majalisar Amurka wacce dama sun taba yi wa Bajemine Natanyahu tafi alhali shi ne mafi girman wanda ya tafka laifi aka bil’adama a wannan zamanin.

 A nata bayanin, kungiyar “Popular Front” ta sanar da cewa; Kira irin wannan na a yi wa fararen hula kisan kiyashi b,a shi da banbanci da mafi munin laifukan da ‘yan Nazi su ka tafka.”

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: majalisar Amurka

এছাড়াও পড়ুন:

Lauyoyin Majalisar Dattawan Nijeriya Sun Ƙaryata Natasha Kan Cewa Kotu Ta Ce Ta Koma Bakin Aiki

A ƙarshe, lauyoyin Majalisar sun ja hankalin lauyoyin Sanata Akpoti-Uduaghan da su yi taka-tsantsan don kauce wa yi wa kundin tsarin mulki kutse ko sanya rikici a majalisa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce; An Rusa Hanyar Tattaunawa da Iran Kan Shirin Na Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima
  • Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi
  • Lauyoyin Majalisar Dattawan Nijeriya Sun Ƙaryata Natasha Kan Cewa Kotu Ta Ce Ta Koma Bakin Aiki
  • China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS
  • Malamin Addinin Musulunci Yayi Kira Da Ayi Gaggawa Gyaran Hanyar Zamfara
  • Falasdinawa Kimani 635 Amurka da HKI Suka Kashe A Cibiyoyin Karban Abinci A Gaza
  • Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha
  • Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha
  • Majalisar Jihar Jigawa Ta Bukaci Karamar Hukumar Roni Ta Samar Da Karin Ajujuwa Ga Fulani Makiyaya