Gwamnatin Sudan Ta Yi Allah Wadai Da Sabbin Takunkuman Da Amurka Ta Kakaba Mata
Published: 25th, May 2025 GMT
Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa: Sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata, bakar siyasa ce ta nemen bata mata suna
A cikin wata sanarwa da gwamnatin Sudan ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba mata sabbin takunkumai, tana mai bayyana hakan a matsayin maimaita kura-kurai irin na baya kan yadda gwamnatocin Amurka suka tafiyar da harkokin Sudan cikin kura-kurai.
Sanarwar ta kara da cewa: “takunkuman da Amurka ta fitar, zarge-zarge ne da suke neman bata sunan kasar da murguda gaskiyar lamari; inda ta ci gaba da bayyana cewa: “Amurka tana ci gaba da bin manufofin da ke kawo cikas ga hanyar da al’ummar Sudan ke bi wajen samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.”
Gwamnatin Sudan ta jaddada cewa: “Takunkuman da Amurka ta kakaba wa sojojin ne bayan nasarorin da suka samu a fagen yaki da suka hada da sauya gaskiyar yakin.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
Fitattun dalibai akalla 12 ne daga makarantun gwamnati suka samu guraben tallafin karatun sakandare a ƙarƙashin Asusun Tallafin Karatu na Jihar Kwara (Kwara-ETF).
A wajen taron gabatarwa ga waɗanda suka fara cin moriyar shirin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa ci gaban harkar ilimi a Najeriya abu ne mai tsada kuma ya zama wajibi kowa ya bayar da gudummawarsa.
Ya roƙi masu masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen gina makarantu ko kuma su ɗauki nauyin daliban da suka nuna bajinta da jajircewa a harkar karatu.
A cewarsa, an zabo daliban 12 ne sakamakon bajintar da suka nuna a matakai daban-daban na tantancewa da Kwara ETF ta gudanar.
Gwamnan ya bayyana cewa tallafin ya kunshi dukkan kuɗin da ake buƙata a karatun sakandaren daliban.
“Muna kira da jama’a su ba da gudummawa da kuma ɗaukar nauyin ɗalibai. Kada a bar wannan aiki ga gwamnati da iyaye kadai. Ilimantar da ‘ya’yanmu hakki ne da ya rataya a kanmu gaba ɗaya,” in ji Gwamna.
Ya yaba da tsarin zaɓen kuma ya taya waɗanda suka yi nasara murna.
A nata jawabin, Babbar Shugabar Kwara ETF, Oluwadamilola Amolegbe, ta ce daliban 12 sun fito ne daga cikin jerin ɗalibai 640 da aka fara tantancewa bisa cancanta.
Ta bayyana cewa tsarin zaɓen ya fara ne da rubuta jarabawa ga dukkan daliban firamare na aji shida da suka amfana da shirin KwaraLEARN na koyon fasahar zamani, har zuwa lokacin da aka kammala tantancewa.
Ali Muhammad Rabi’u