Aminiya:
2025-09-17@23:17:18 GMT

Gwamnatin Gombe za ta taimaki ’yar shekara 14 da aka yi wa auren dole

Published: 25th, May 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Gombe, na shirin taimaka wa wata yarinya ’yar shekara 14 da aka tilasta yi mata auren dole a Jihar Taraba.

Kwamishinar Ma’aikatar Mata da Walwala, Asma’u Iganus, ta ce yarinyar ta nemi taimako bayan da kakanta ya ɗaura mata aure da wani mutum a matsayin mata ta huɗu.

An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja Jami’an Sibil Difens sun bude wuta a garin Jos

Ta ce hakan ya ci zarafin yarinyar kuma gwamnati ba za ta zuba ido ba.

“Mun fara ɗaukar matakan kare ta. Mun tuntuɓi kotu kuma lauyoyin gwamnati za su shiga shari’ar don kare ta,” in ji Asma’u.

Ta ce yarinyar ta ce tana son ci gaba da karatu, don haka gwamnati za ta saka ta a cikin tsarin shirin AGILE domin ta koma makaranta.

Haka kuma an ba ta tallafin kuɗi, abinci da kayan amfani don rage mata wahalhalu.

Lauyar Ma’aikatar Shari’a, Barista Marilyn Na’omi Abdu, ta ce za su yi iya ƙoƙari wajen kare yarinyar a kotu.

Yarinyar ta ce asalin ta daga Gombe ta ke, amma suna zaune a Taraba inda mahaifinta ke noma.

Ta ce kakanta ya tilasta yi mata auren wani mutum mai kuɗi ba tare da amincewarta ba.

“Ina zaune kawai sai aka ce an ɗaura min aure. Ban san shi ba kuma bana son shi,” in ji ta.

Ta ce mijin yana azabar da ita, har ɗaure ta yake da ƙarfi kafi kafin ya sadu da ita.

Ta nuna yadda ya ji mata ciwo a hannunta a matsayin shaida da irin dukan da ta ke sha.

Daga ƙarshe, ta gudu zuwa Gombe don neman taimako.

Gwamnatin Gombe, ta ce za ta ci gaba da kare yara mata da faɗakar da jama’a kan illar auren dole.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamnati Taraba yarinya

এছাড়াও পড়ুন:

An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe

Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.

Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.

Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Ya ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”

Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.

A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.

Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja