Leadership News Hausa:
2025-07-08@18:21:31 GMT

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)

Published: 24th, May 2025 GMT

Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (2)

 

Tsarin ilimin da ba sai an je makaranta ba

Irin wannan nau’in ilmin shi ba tsara shi ake yi ba, hakanan ma ba yana bin wani abinda aka shirya bane dangane da koyarwar. Irin wannan ilimin baya bukatar wani adoI wato ilimin da a ciukin ajin dake makaranta ake koyon shi ba. A waje n eake koyon shi wato manufa ba a wata makaranta ba wadda ake koyarwa domin a samu shi ilimin.

Wannan kuma yana faruwa ne idan mutane suka samu karuwa da wasu dabaru ko ilimi daga gida, dakin karatu, ko kum wata kafar sadarwa ta na’urar waya da duk wani abinda za’a iya amfani da shi domin hakan.Bugu da kari irin wannan ilimin ana iya samun shi daga wurin Shugabannin al’umma.

Kasancewa cikn al’umma ta wannan hanya ko waccan irin hakan ma wata hanya ce da mutum yake karuwa da nau’in ilimin da ba sai an je makaranta ba an zauna, a aji. Irin wadancan Malaman ai Iyaye ne, ‘yan’uwa, da kuma makwabta, da wasu al’umma wadanda su sun koya ne daga irin dabarun da suka koya a rayuwa,daga iri yadda mutum zai sa kaya/sutura da anau’oin Bukukuwa ko wasu raturruka, yadda za a sayo abubuwan hadawa ayi abinci,da kuma yadda za’a lura da tsaftar jiki.

Sai dai kuma akwai wasu abubuwan da suke nasaba da yadda al’adu suke yaduwa,yayin da abin kan faru ta wani yanayin da ba ayi tsammani ba,yana iya kasancewa irin ilimin a ake karuwa da shi ba sai an je makaranta ba.Ya dangata ko dogara da yadda al’umma suke tafiyar da al’adunsu,yadda suke yi na’am da su,da kuma yadda halayen zamantakewa suke.

 

Ilimin da ya hada da nau’oin ilimi biyu

Shi iri wannan nau’in ilimin ya sha bamban da guda biyun domin abin ya danganta ne da irin salon da yake tafe da ita koyarwar ta kunsa.Shi yana da irin na shi tsarin kai tsaye kuma,amma shi ma ba a makaranta ba ake iya koyon shi ba.Akwai tsarin yadda yake wanda ba mai rikitarwa ba,babu kuma wani lamarin kayyade shekaru.

Alal misali akwai irin wuraren da ake koyon shi wadanda suka bambanta da guda biyun, koyon sana’oi wuraren da ake koyar da su, tsarin horarwa mai gajeren zango,irin na Shugabannin Kamfanoni wadanda ba wai sai kwararru ba wadanda suka samu ilimin ta irin nau’in ilimin da ake koyar da shi a cikin aji.

 

Me yasa ilimi yake da muhimmanci?

Me yasa ilimi yake da muhimmanci?Ilimi yana da muhimmanci saboda dalilai masu yawa. Ta hanyar ilimi mutane/ al’umma suna koyon yadda za suyi karatu, rubutu, da kuma saurare. Gaba daya lamarin ilim har ya kunshi rayuwar abubuwan da mutum yake son cimmawa a gaba.Mutanen da suke da ilimi mai zurfi irin sune ake rubibinsu a wuraren da ake daukar ma’aikata inda kuma albashinsu ya kan kasance mai tsoka. (Abulencia, 2021) Hakananma shi ilimi yana maganin fatara, da yunwa, inda yake bada damar yadda mutum zai samu ci gaba. Irin hakan ce ta sa Iyaye suke kokarin sai ‘ya’yansu sun je makaranta, yayin da ita kuma gwamnati take taimakawa ta hanyoyin da za su sa dukkanin yara da manya sun samu da karuwa da ilimin. (UNESCO, 2011)

Bayan haka ma ilimi yana taimakawa ‘yanmata da mata wajen samun dama wadda ba za a samu rata mai yaw aba tsakaninsu da maza.Ta haka ne aka samu rage yawan yaran mata kanana ke daukar ciki da kashi 6 cikin 100, saboda karun shekarun da ‘ya’ya mata suke yi wajen karatu kamar yadda Bankin duniya ya bayyana.Ita ma Hukumar dake karkashin majalisar dinkin duniya da ake kira UNESCO,mai kula da lamurran ilimi, kimiyya, da kuma al’adu ta gano cewa jaririn da mahaifiyarsa ta iya karatu yana kashi 50 na yiyuwar samun damar kaiwa har zuwa shekara biyar,wannan ya nuna ilimi ya taimaka wajen irin yadda kananan yara suke mutuwa kafin su kai shekara biyar.

Sai dai kuma wani nazarin da aka yi ya nuna an samu koma- baya wajen samun amsar tambayar me yasa ilimi yake da muhimmanci ga samun nasara? A wani rubutu mai taken “Amfanin abokantaka /’yan’uwantaka tsakanin ilimi da tattalin arziki,halayya da kuma matsayin abin a siyasance wanda”International Journal of Social and Management Studies,Deak and Tanama ya wallafa, a shekarar(2021)ya bayyana cewa “Idan aka samu matsalar rashin yin shiri da tsarin ilimi wanda ya kamata yana sanadiyar haifar da manyan matsalolin da suke da amfani idan tun farko an yi su saboda kaucewa aukuwar irin hakan: rashin aikin yi,aikata laifuka,shan muggan kwayoyi,idan ana maganar ci gaban gwamati ne ta bangaren tattalin arziki,a hanyoyi da dama hakan ya ta’allaka ne kan taimakon da take samu daga kimiyya da kuma fasaha.’’Don haka shi yasa ilimi yake da amfani/ muhimmanci ga ko wadanne al’umma,da daidaikun mutane’’.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima

Haka kuma ya yaba da irin rawar da shugaba Bola Tinubu ke takawa wajen tallafa wa zaman lafiya ta hanyar hana yaɗuwar irin waɗannan makamai.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi: Ana Kokarin Rubuta Sabon Babi Na Zamanantar Da Sin A Lardin Shanxi
  • An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi
  • HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
  • Nijeriya Ba Ta Da Sha’awar Yin Gwajin Makamin Nukiliya — Shettima
  • Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
  • An Kaddamar Da Shirin Samar Da Wutar Lantarki A Jami’ar Kashere Gombe.
  • Kano ta sami rahoton cin zarafin yara 351 – NHRC
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a?
  •  Togo: An Yi Kiran Sake Yin Wata Sabuwar Zanga-zanagr Kin Jinin Gwamnati
  • Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau