Gobara ta ƙone ofishin zaɓe INEC a Sakkwato
Published: 14th, February 2025 GMT
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki.
Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa.
A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin jihar, Hauwa Aliyu Kangiwa ta ruwaito.
Ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Talata 11 ga watan Fabrairun 2025.
“Duk ginin ofishin ya lalace. Kayayyakin da suka lalace sun haɗa da tebura da kujeru da kayan aiki da kayan zaɓe da ake iya ɗauka, daga cikinsu akwai akwatunan zaɓe 558, rumfar kaɗa ƙuri’a 186, jakunkuna 186 na zaɓe da kuma kayayyakin da suka haɗa da manyan tankunan ruwa guda 12 (litta 1,000), tabarmin barci 400 da bokitan robobi 300.
“Rahoto na farko daga ofishinmu na jihar ya nuna cewa an samu ƙaruwar wutar lantarki kafin faruwar lamarin,” in ji Olumekun.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA