Gwamnatin kasar Amurka ta ce bata bukatar samuwar jkadan kasar Afrika ta kudu Ebrahim Rasool a kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Jumma’a, ya kuma kara da cewa Rasool mutum ne wanda yake nuna wariya, yake kuma kin Amurkawa.

Don haka bama da abinda zamu tattauna da shi, kawai bama son ganinsa a cikin kasar babba.

Rubio bai bayyana dalilan daukar wannan matakin a kan jakadan ba, amma hakan ya faru ne bayan da Jakadan Rasool ya wata cibiyar bincike na Afrika ta kudu inda a jawabin da ya gabatar ya zargi shugaban kasar Amurka Donal Trump da, da samar da shirin “sake maida Amurka kasa babba” da wani shirin fifita fararem Amurka  a kan sauran mutane a duniya.

Labarin ya kara da cewa tun lokacinda Trump ya sake dawowa fadar white house aka hana jakadan Afirka ta kudu a kasar ganawa da jami’an fadar white House kamar yadda ya dace. Fakon haka Amurka ta yi barazanar dakatar da tallafin da take bawa kasar Afrika ta kudu saboda karar da ta shigar kan HKI wacce ta aiwatar da kissan kiyashi kan Falasdinawa a Gaza daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 har zuwa yanzun. Banda haka kasar ta sami goyon baya daga kasashen duniya da dama. Kuma gwamnatin Amurka ta bukata Afirka ta kudu ta janye karar amma taki amincewa.

Ya zuwa yanzu dai kotun ta ICC ta fidda sammacin kama Firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yauf Galant. Kafin haka dai Ebrahim Rasool ya taba zaman jakadan Afrika ta kudu a kasarAmurka daga shekara ta 2010-2015 a lokacin shugabancin Barak Obama

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa tsakanin Amurka da JMI sun lalace ne saboda zagon kasar HKI da farwa kasar da yaki. Yace gwamnatin Amurka idan tana so zata farfado da shi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani rubutun da yi wa jaridar ‘Financial Times ta Amurka. Inda y ace : Har yanzun JMI tana bukatar hanyar Diblomasiyya, amma kuma hakkinta ne mu yi shakku a kan ninyar Amurka niyyar Amurka a tattaunawa da ita. Idan Amurka da gaske take ta nuna cewa ta warware wannan matsalar to tana iya yin haka da adalci.

Sai dai, inji ministan, yakamata Amurka ta san cewa al-amura sun sauya kuma bayan wannan yaki na kwanaki 12 da HKI da ita suka kaiwa cibiyoyin makamashin nukliyar har guda uku ta kuma kashe manya-manyan Janaral na sojojinmmu sannan ta kashe masana fasahar nukliyammu da kuma wasu Iraniyawa.

Aragchi ya ce: Iran ba zata mika kai kamar yadda Amurka take riyawa ba. Iran kasashe wacce tayi shekaru dubbai a duniya, kuma ta kutsa yake-yake da dama a baya ta kuma sami nasara. Sannan yace: Muna son zaman lafiya a ko yauce, amma mune muke iya tabbatar da ita ko mu hanata tabbata.

Yace: A halin yanzun kuma ba zamu taba amincewa da kissam mutanemmu ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Aragchi: Amurka Tana Iya Farfado Da Tattaunawa Kan Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Idan Tanaso
  • Amurka Tana Fatan HKI da Hamas Su Tsaida Budewa Juna Wuta Na Kwanaki 60 A Karshen Wannan makon
  • Kasar China Ta Yi Watsi da Barazanar Trump Na Kakabawa Kasashen BRICS Karin Takunkuman Tattalin Arziki
  • HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-Haren HKI Kan Kasar Yemen
  • Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12
  • China Ta Maida Martani da Haka Kayakin Kiwon Lafiya Na Tarayyar Turai Shigowa Kasar
  • Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
  • Yankin Kudu-Maso-Kudu Zai Cimma Matsaya Ɗaya Kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki – Sanata Dickson
  • Masanin Kenya: Kasashe Masu Tasowa Suna Bukatar Kasar Sin