Karkush: Ganawata Da Arakci A Tehran Ta Yi Kyau
Published: 15th, March 2025 GMT
Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau.
Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma aiki tare.
Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu, da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Sharia A Nan Iran Zata Bayyana Abinda ya farsu A Tashar Jiragen Ruwa Na Shahid Rajae
Kakakin ma’aikatar sharia a nan JMI ya bada sanarwan cewa,ma’aikatar za ta bayyanawa mutanen sakamakon bincken da suka gudanar kuma suke ci gaba da yi, dangane da fashewa da kuma gobatar da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Shahid Rajaee a cikin yan kwanakin da suka gabata. .
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran, ya bayyana cewa, Asgar Jahangir kakakin ma’aikatar sharia da kuma Zabihullah Khudayiyan shugaban hukumar bincike ta kasa, sun gudanar da taron hadin guiwa da yan jaridu da kafafen yada labarai na cikin gida da waje a safiyar, dangane da fashewa da kuma gobarar da ta biyo baya a tashar jiragen ruwa na Shahid Rajaee.
Banda haka jami’an sun amsa tambayoyin yan jarida bayan jawabansu dangane da hatsarin wanda ya lakume rayukan mutane, fiye da 70 da kuma jikata wasu kimani dubu guda.
Kafin haka dai jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaee ya bada umurni ga ma’aikatun biyu su gudanar da cikekken bincike don gani musabbabin wannan hatsarin sannan idan akwai wadanda suka da hannu, ko sakaci a cikinsa, a bi tsarin da ake da shi don hukunta wadanda suke da laifi.