Aminiya:
2025-11-03@08:56:21 GMT

Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC

Published: 4th, July 2025 GMT

Kusoshin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sun shiga haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC da nufin kayar da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC.

Tsofaffin mukarraban gwamnatin Buhari da suka koma haɗakar ADC sun haɗa da tsofaffin ministoci da tsofaffin gwamnoni da masu muƙaman siyasa.

Yawanci sun raba gari da APC ne saboda zargin an yi musu rashin adalci a jam’iyyar da kuma gazawar Gwamnatin Tinubu wajen magance matsalolin da ke ci wa ’yan Najeriya tuwo a ƙwarya.

1- Nasiru El-Rufai

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na gaba ne a tafiyar haɗakar inda tun farko ya lashi takobin ƙalubalantar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027.

NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta? Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan

Fara maganar haɗakar ke da wuya aka ga El-Rufai a gidan Buhari da ke Kaduna, inda ya sanar da ficewarsa daga APC.

Daga bisani El-Rufai tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da wasu jaga-jigan ’yan APC a gwamnatin Buhari suka ziyarci shugaba kasan.

An yi zargin sun je ne domin neman albarkarsa domin ya amince wa ’yan tsohuwar jam’iyyarsa ta CPC su fice daga APC su shiga haɗakar.

2- Abubakar Malami

Ministan Shari’a a wa’adi biyu da Buhari ya yi, ya sanar da ficewarsa daga APC da kuma aniyarsu ta yaƙar Gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027 saboda ta jefa ’yan Najeriya cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da kuma gaza magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki.

Tsohon ministan shari’an, kuma wanda tsohon wanda a baya ya nemi takarar Gwamnan Jihar Kebbi, an lura ya yi baya-baya a harkokin APC tun bayan hawan mulkin Tinubu.

3- Hadi Sirika

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama a zamanin Buhari, dan asalin Jihar Katsina ne, wato mahaifar tsohon shugaban ƙasan.

Hadi Siriya sun jima da taba da raba gari da Gwamnatin Tinubu kuma a halin yanzu yana fuskantar shari’a kan zargin karkatar da kuɗaɗen kwangila da sauran zarge-zarge a ma’aikatar sufurin jiragen sama.

4- Rotimi Amaechi

Tsohon Ministan Sufuri a zamanin Buhari, kuma tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana aniyarsa ta fitowa takarar shugaban ƙasa a ADC.

Amaechi kamar takwarorinsa da suka fice daga APC bisa zargin an yi musu ba daidai ba, na zargin gwamnatin Tinubu da gazawa.

5- Rauf Aregbesola

Tsohon Gwamnan Jihar Osun wanda Buhari ya naɗa Ministan Harkokin Cikin Gida, tsohon na hannun daman Tinubu ne.

A halin yanzu shi ne ADC ta nada a matsayin Sakataren Jam’iyya.

6- Solomon Dalung

Tsohon Ministan Wasanni ya daga cikin waɗanda suka shiga wannan haɗaka ta ADC.

Ko da yake wa’adi daya kadai Dalung ya yi minista a zamanin Buhari, ida gaba bisani ya koma sukan kamun ludayin gwamnatin.

Bayan shafe watanni ana tattaunawa kan haɗakar jam’iyyun adawar ne dai a ranar Laraba suka ƙaddamar da shugabannin riƙo a ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark.

Haka kuma sun naɗa tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren riko na ƙasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buhari Tsohon Gwamnan Jihar tsohon Gwamnan Jihar Gwamnatin Tinubu gwamnatin Tinubu a gwamnatin

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida