Aminiya:
2025-07-04@05:50:29 GMT

Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar

Published: 4th, July 2025 GMT

Majalisar riƙon ƙwarya ta Gwamnatin Mali ta bai wa Shugaban Mulkin Sojin ƙasar, Janar Assimi Goita, wa’adin mulki na shekara biyar, wanda za a iya sabunta shi fiye da sau daya ba tare da zaɓe ba.

A bara ne Janar Goita ya yi alƙawarin maido da mulkin dimokuradiyya a ƙasar, sai dai hakan ba ta samu ba.

Tsohon golan Super Eagles, Peter Rufai ya mutu Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad

Wannan matakin ya bude hanya ga Janar Goita ya ci gaba da jagorantar kasar ta yammacin Afirka har zuwa aƙalla shekarar 2030, duk da alƙawarin da gwamnatin sojan ta yi na komawa mulkin farar hula a watan Maris na shekarar 2024.

Sai dai sabon ƙudirin dokar ya yi tanadin cewa Goita zai ci gaba da mulki har zuwa lokacin da ƙasar za ta daidaita.

Majalisar riƙon ƙwaryar wadda ke da mambobi 147, ce ta amince da ƙudirin, kuma yanzu yana jiran Janar Goita da kansa ya sa hannu domin ya zama doka.

A 2021 ne Janar Goita ya hau karagar mulkin ƙasar a wani juyin mulkin soji, inda ya alƙawarta magance tashe-tashen hankulan masu iƙirarin jihadi.

Sai dai har yanzu mayaƙan na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare, inda a baya-bayan nan ma suka kai hare-hare kan sansanonin sojin ƙasar tare da kashe sojoji masu yawa ciki har da sojojin hayar Rasha

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Janar Goita

এছাড়াও পড়ুন:

Baltasar: Mutumin da ya fitar da bidiyon lalatarsa da mata sama da 400 ya gurfana a kotu

Baltasar Engonga Ebang, mutumin nan dan kasar Equatorial Guinea da a bara ya saki bidiyon lalatarsa da mata sama da 400 na fuskantar shari’a a kotu kan badakalar kudade.

Baltasar, wanda tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta kasar Equatorial Guinea ne dai an gurfanar da shi a gaban kotu ne bisa zargin karkatar da kudade a karkashin Ma’aikatar Kudin kasar.

Masu shigar da kara na neman a yanke masa hukuncin daurin shekara 18 a kurkuru sannan a umarce shi ya dawo da wasu kudaden masu yawa.

’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar TIinubu – Amaechi Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota

Ana dai zarginsa ne da almundahana, azurta kai da kuma rub-da-ciki a kan dukiyar al’umma lokacin da yake rike da mukamin hukumar.

Lauyoyi masu shigar da kara na zargin Baltasar da yin babakere a kan kudi har sama da CFA biliyan daya, kwatankwacin sama da Naira biliyan biyu da rabi.

Bugu da kari, lauyoyin na kuma son a yanke masa hukuncin shekara takwas kan laifin almundahana, shekara hudu da wata biyar kan laifin azurta kai, sai kuma shekara shida kan laifin cin amanar ofishinsa.

Lauyoyin sun kuma bukaci kotun ta ci Baltasar tarar CFA miliyan 910 sannan a haramta masa rike kowanne irin ofishin gwamanti na tsawon lokacin da zai shafe a dauren.

To sai dai lauyoyin wanda ake karar sun yi fatali da dukkan laifukan da ake zargin wanda suke karewa da aikatawa da ma sauran wadanda ake zargin, inda suka ce bas u da tushe.

A watan Disambar bara ne dai bidiyoyin Baltasar na lalata da mata sama da 400 suka cika shafukan sada zumunta. Daga cikin matan da aka gan shi yana lalata da su har da matan ministotin kasar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Jigawa Ta Isa Roni A Ci Gaba Da Rangadin Kananan Hukumomi
  • ‘Yan Sanda Sun Hana Yunqurin Fasa Shago a Gombe, Tare da Kwato Babur
  • ’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC
  • Baltasar: Mutumin da ya fitar da bidiyon lalatarsa da mata sama da 400 ya gurfana a kotu
  • Ben Gafir Ya Bukaci Gwamnatin HKI Ta Mamaye Yankin Gaza Gaba daya
  • Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba
  • Aragchi: Hare-Haren HKI Ya Kara Rashin Zaman Lafoya A Yankin Yammacin Asiya
  • Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare
  • Xi Jinping Ya Jaddada Niyyar Gina Babbar Kasuwar Kasa Ta Bai Daya, Tare Da Raya Tattalin Arziki Na Teku Mai Inganci